Abban Sojoji Book 3 Takun Karshe Complete New Page By Boss Bature

 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋







𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇


https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1





قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤

𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠


*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*




_Ga masu karanbanin haɗa mun document,koda gigin wasa kada wanda ya kuskura Ya ƙara haɗamun document,kuma bazaku ta6a samun Complete document na takun ƙarshe ba,saboda ba yanzu zan haɗa shi ba koda na kammala littafin,Dole sai a wurina za'a same shi from page one to the end,if not babu wanda zai baku shi cikakken shi,Sannan Zan canza Lokacin posting_






Lokacin dana fara aiki acikin gidan nan,mahaifinku ya mayar dani tamkar ba ƴar aiki ba don alokacin ya tambayeni game da mahaifin yarona,na sanar dashi cewa ya rasu dalilin hadarin mota,daga haka kuma na kulle bakinshi don kar ya nemi jin wani bayani agame da dangina,Ya ɗauki Haroon ɗansa,Kuma Ya nuna yana so inbar mashi haroon ya kasance acikinku,baya son Ya taso a matsayin bare,Ba ƙaramin daɗi naji ba,Duk da mummunan ƙudirin da nake dashi,


Tsawon Lokaci da fara aikina cikin gidan nan,na fara shirya maku maƙarƙashiya,da niyyar tarwatsa farin cikin gidan nan,Amma silar kyautatawar da mahaifinku keyi mun da kuma wasu daga cikinku yasa na ɗan dakata,Akwai wani hadithi da manzon Allah (SAW) yake cewa"Jubilatul ƙulubu ala hubbi man ahsana ilaiha,Wabugudi man Asa'a ilaiha,(An halicci zuciya da Son mai kyautata mata da kuma ƙin mai munana mata),Wannan kyautatawar da kuke Yi mun ita ta Jani har izuwa tsawon lokacin nan Batare dana Aiwatar da abunda ya kawoni cikinku ba,a lokacin banyi tsammanin zan faɗa tarkon son wani acikinku ba,Sai gashi na kamu da tsananin Son mahaifinku,Saboda yafi kowa kyautatamun,Ya yarda dani sosai Kuma ya damu dani akan kowa na cikin gidannan,Da yake ita zuciya ba ƙashi ne da ita ba,bansan lokacin dana afkawa Sonshi ba,sai kuma na fara kishi da Alexandra,don nasan cewa muddin tana acikin gidan bazan ta6a samun soyayyar mahaifinku ba,Wannan dalilinne Yasa nayi Amfani da sihirina wurin Ƙuntata mata,ta fara jin ƙunci acikin ranta,Zaman Nigeria ya gagareta,babu arziƙi ta tattara tabar ƙasar nan,batare da ta ƙarasa shayar da Junaid ba,ta barshi cikin tsummanshi yana ɗan jinjirinshi.......... "


Bata ƙarasa maganar ba,Sakamakon wani irin kukan Kura Da Mommy tayi takai mata damƙa a wuyanta,Muryarta adisashe take magana hawaye na zuba"Amma kin cutar dani Azmee,Kin cuci rayuwata,Da kuma rayuwar Junaid,Ashe kece silar dana tafi nabar mijina da ƴa'ƴana,I will neva forgive you....."kasa ƙarasa maganar tayi,nan take ta fashe da kuka,Daƙyar Abba ya samu ta saki wuyan Azmee,har tangal tangal tayi zata faɗi da sauri Jahan ya ruƙota,Ya taimaka mata ta zauna saman hannun kujera tana kuka"matar nan tajima tana cutar da rayuwarmu,Dama ance makashinka Yana tare dakai"Sosai take kuka,Ita kanta Azmeen kukan takeyi,Su Sehrish da Jahad dukkansu kuka sukeyi,Oummansu ma idanuwanta cike tab da kwalla,

Bayan ta tsagaita da yin kukan taci gaba da cewa"A lokacin mahaifinku Ya ɗauki Junaid ya bani shi don inci gaba da shayar dashi,babu yarda Hajiya azeema batayi ba akan Ya bata Junaid ta shayar dashi,Amma ya nuna cewa yafison na shayar dashi,Ba don komai ba Sae don baison Junaid Yayi nisa dashi,tunda ita a lagos take zaune,bayan ya damƙamun Amanar Junaid,naci gaba da shayar dashi,Allah shine shaidata,Inason Junaid sosai,Fiye da son da nake yi ma haroon,Sai na dinga ji kamar ni na haifeshi,har banso su Fawan suzo ɗaukarshi,gashi lokacin haushina suke Ji saboda ina ƴar aiki ƙasƙantacciya an bani Ƙaninsu ina shayarwa,ni kuwa daɗi na dinga Ji,Saboda ina tunanin ta hanyar Junaid zan samu soyayyar mahaifinku don tsakani da Allah nike sonshi hakan yasa banyi mashi wani sihiri ba wai don ya so ni,babu wanda yasan Inasonshi,Sae Laila matar Ishaq da yake ƙawatace duk da ba wani shiri nake da ita ba,Amma ina neman shawara awurinta,haka Hajjaju ma muna mutunci da ita,Dukkansu babu wanda yasan Ainihin wacece Ni,Duk irin son da nake yi ma Abbanku bai ta6a lura ba,Naso na sanar dashi amma ina tsoron Yace baiso na,bansan wani hali zanshiga ba,Lokacin da Junaid Ya fara tasawa,abunda Ya bani tsoro dashi irin wayon dake gare shi,Kullum agabanshi nake yin waya cikin harshen fulatanci,kwatsam wata rana,bayan na kammala waya,sai yake ce mun ae Yaji duk abunda nace,A lokacin na ɗauka da wasa yake yi don nasan baijin fulatanci,Sai cewa nayi toh ya faɗamun me nake cewa acikin wayar,ba zato ba tsammani Yaron nan Ya fassara mun maganganun da nayi acikin wayar,hankalina yayi mugun tashi,Ko makaranta ba'a sanyashi ba,na ruƙe shi ina tambayarshi a ina ya koyi harshen fulatanci,Sae ce mun yayi a wurina yaji ina yi,duk in zanyi waya,tunda naji haka saina tsorata dashi,tabbas wata rana zai iya tona mun asiri,tunda har ya iya yaren da nake yi wanda a waya kawai nake magana da harshen,Kawai na yanke shawarar In juye mashi tunaninshi ta yadda bazai ta6a fahimtar komai ba,Tun daga wannan lokacin Junaid Ya zama soko,Bai ɗaukar karatu ko mis'ƙala zarratin,Nasan na cuci Junaid,Da ace Yayi ilimi da ina da tabbacin cewa zai kasance ɗaya daga cikin ƴaran da duniya zatayi alfahari dasu saboda baiwarsu,A kwana a tashi,Rana ta farko dana fara Yin tozali da Rafayet,Bazan ta6a mantawa da wannan Lokacin ba,dawowarshi kenan daga U.S,Ya soma tambayar ina Babyn da Mommynsu ta bari,Su fawan ke sanar dashi cewa Yana a wurin mai aikinsu har suke bashi labarin cewa ni na shayar dashi,Ranshi yayi mugun 6aci Yasa su kirani,Na fito ɗauke da Junaid a hannuna,ya rufesu da faɗa don me za'a ba mai aiki ta shayar da ƙaninsu,sun tabbatar da tsaftar jikina ne,A karshe ya kar6e Junaid daga hannuna,Ya wuce dashi dakinshi,


Tunda na koma ɗaki,na kasa runtsawa saboda tunanin Rafayet,Kyawun fuskarshi dana surarshi suka ɗebeni har na Fara kamuwa da sonshi,Maimakon da yayi mun faɗa inji haushinshi,Sai ma sonshi da nake kara Yi,na kasa samun natsuwa kullum in naje kai mashi abinci,ban iya kawar da idanuwana daga kallonshi,shi kuwa bai ta6a ɗago da idonshi ya kalleni ba a wannan lokacin balle insa ran zan same shi........."dakatawa ta ɗanyi da yin maganar,Yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta,

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,Kallon Sgr kawai take yi,Shi kanshi abun ya ɗaure mashi kai,bai ta6a sanin wannan zancen ba,Mommy kuwa wani irin kallo take binta dashi,


"Daƙyar na samu Sgr ya fara tanka mun in na gaishe shi,Ba ƙaramin daɗi nake ji ba idan na kai mashi abinci yaci,ni kaɗai nayita haukan soyayyata don shi baisan ma inayi ba,A kwana a tashi Ya koma U.s A ranar kamar nayi hauka,bayan tafiyarshi na soma tunanin Me ya kawoni gidan?Me nake jira da ban aiwatar da mummunan ƙudurin daya kawoni ba,Saboda jin daɗin da nake ciki,Na manta cewa ɗaukar fansa ta kawoni gidan,Komai na more rayuwa ina samu,Inci me kyau in sha me kyau in kwana a me kyau,ga Albashin da Abba ke bani harya zarce na wani likitan,ko lokacin bani albashina baiyi ba,Yana yawan dunƙulo kuɗi ya damƙa mun,Yace ga wannan in ina buƙatar wani abu,Insa driver yakaini kasuwa inyi siyayya,Wani irin daɗi nake ji,koba shi ba da yawan lokutta Yusuf Yana bani kuɗi hakanan kyauta yace mun ga wannan Inyi amfani dasu,Ganin irin ƙaunar da suke nuna mun saina fara tunanin kodai in janye batun ɗaukar fansar nan tawa,Tabbas a lokacin na fara tunanin yin tuba in koma Ga Allah,Amma sai Dangina suka taso ni gaba,Musamman Hamma Ghali barazana Ya soma yi mun akan kodai na aiwatar da abunda ya kawoni cikinku ko kuma zai ɗauki mataki akaina,na tsorata sosai,Saboda mugune shi,nasan shi sarai,kuma shine Shugaban ƙungiyarmu ta matsafa,komai nake Yi acikin gidan nan akan idonshi nake yi,Duk da bamu atare amma Yana da madubin tsafinshi wanda yake kallon duk wani motsina,Ba don naso ba haka naci gaba da bin umarninshi,A lokacin Haroon na soma ƙoƙarin janyowa Jikina,Na nuna mashi cewa ku ba jininshi bane,Ya daina shige maku,Fansa muka zo ɗauka acikinku,Amma sai ya kangaremun,Yace shi bazai yarda a haɗa baki dashi ba,Wurin cutar daku ba,Saboda Abba yana sonshi,kuma Yanayi mashi duk abunda Yake so,Don haka inma naci gaba dayi mashi magana zai tona mun asiri ne,Jin wannan magana ta haroon Yasa na fara tunanin ta yadda zan juye mashi tunaninshi,Don na lura ɗabi'unsa da halayyarsa ba irin ta dangina bace,Duk da dama ina kokwanto akanshi,Banda tabbacin wanene mahaifinshi,Ganin yana nema yafi ƙarfina sai na sanar ma Hamma ghali abunda Haroon Yace,aikuwa tun daga wannan Lokacin da mukayi waya dashi,Ya sanar dani cewa In kawar dakaina akanshi zanga me zai biyo baya,tofa aikoda yace haka,cikin ƴan kwanaki ƙalilan Haroon ya canza,Ya zama mugun ƙarfi da yaji,Wata muguntar ma ba saina sanar dashi ba,dakanshi yake yi,Ga bin mata da bin maza,Shaye shaye duk wani aiki na shaiɗanci Haroon ya iyashi,nikaina banji daɗin Sauyawar Haroon ba,Iya Cuta dai Mun cutar dashi,Duk da bani bace silar jefa shi cikin halin da yake ciki ba,Amma ni mahaifiyarshi ce,dani akayi amfani wurin Canza mashi tunaninshi,su kuma Su twins Rashin kunyar da suke yi mun ne Yasa nayi masu turen shaiɗanin Aljanu ajikinsu,Waɗanda ke sanyasu suna Neman junansu wanda in har basuyi ba,Aljanun nan ke jibgarsu da bulala,........."sosai Azmee ta fashe da kuka,


Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi,wasu ma gaza cigaba da tsayuwa suka yi dole suka zauna,


"About Junaid!Ke da Haroon Waye ya shirya Mutuwarshi"?Sgr ne yayi mata tambayar,

Daƙyar ta tsagaita da Yin kukan ta soma kora mashi bayani,

  "Haroon ne Ya shirya mutuwar Junaid,A lokacin Kun fusata shi sosai,dama a ƙule yake daku,saboda bambancin da kuke nuna mashi don ba ahankalinshi yake duk abubuwan da yakeyi ba,Duk da ni naso In kashe Junaid,ko dan in fanshe haushin kisan Mijina da akayi,Nasha Sanya Haroon ya kashe Junaid,Amma sai ya ce mun bazai Iya kashe shi ba,Junaid yana sonshi sosai,Kuma bai aikata mashi laifin da zai kasheshi ba,Har ce mun yakeyi zai iya kashe kowa acikin gidan nan koda kuwa Abbane,Amma banda Junaid,Ni gaskiya aranar bansan maiya ƙona mashi rai ba,Har ya bada Umarnin akashe mashi Junaid,



a ƙa'ida Miyagun dake yi mana aiki,basa Yanke hukunci in ba sun sanar dani ba,Dole sai in ni na basu umarni kaitsaye suke aiwatar da abu,Haroon ya basu Umarni su kashe Junaid su kuma Sun kirani a waya sun sanar dani cewa Haroon Ya basu Umarnin su kashe Junaid,Shin da sanina koba da sani na ba,"!nan take nace masu karsu kuskura su kashe shi,Su san yarda za'ae su ɗauke Junaid daga cikin motar sannan su ƙonata yarda kowa zaiyi tunanin ya mutu,Nayi hakanne saboda banaso Haroon yaji cewa Na hana su bi umarninshi don zai canja wata hanyarne,sannan Kuma Don Junaid Ya zame mun makamin da zan Yaƙe ku dashi,


Ƙarin bayani,


Lokacin da Jahad ta fita daga cikin motar ta tsallaka zata siya masu ice cream,Junaid Ya dinga ƙwala mata kira,Ta dinga juyowa tana kallonshi Yana yi mata bye bye,bayan mai ice cream ɗin ya sallami mutanan dake gabanshi,Yace ma Jahad madam guda nawa za'a baki,Ta juya ta bashi Amsa,A cikin wannan Lokacin kafin Jahad ta lalubo kuɗi acikin jakarta ta miƙa mashi,adai dai lokacin,waɗannan miyagun suka buɗe motar,kafin Junaid ya ankara suka shaƙa mashi cocaine a hancinshi gaba ɗaya ya fita hayyacinshi,janyoshi su kayi daga cikin motar da hanzari suka fitar dashi,wanda ya ɗauki Junaid a kafaɗarshi ya juya dashi ta baya inda suka ajiye motarsu ya tura shi aciki,Shi kuma ɗayan Ya jefa bomb acikin motar,Yana barin wurin,Gingimarin Motar nan Ta shararo da gudu,Dama already sun kira wayarshi yana akan layi suna sanar dashi cewa Babu Yaron acikin motar,Atsiyace Yabi takan motar Junaid Ya rugurguzata,Yana sauka ya antaya da gudun gaske,Nan take Bomb ɗin cikin motar Ya fashe,Dama sun ɗibar mashi adadin mintunan da zai tashi,To masu karatu Kunji yadda akai Junaid Ya tsira,Baya acikin motar lokacin da suka take motar,Ko lokacin da Jahad ke ihu tana kuka,Duk a kunnanshi bawan Allah,Yana acikin motarsu sun rufe shi,Sam baya acikin hayyacinshi sai faman shafa glass ɗin motar yake yi yana kallonta,A haka har suka tashi motar da gudu suka bar wurin bayan sun dauki vedion motar naci da wuta wanda suka tura ma haroon,


Yadda akai Sgr yasan game da abubuwan daya fadi ma haroon kuwa,dama tun farko,ya dawo Nigeria ne da niyyar yin bincike,don Mommynsa tasha fadi masa cewa akwae abubuwan dake faruwa ba daidai ba acikin gidan,kuma ta sanar dashi ita bata yarda da azmee ba,wannan dalilinne yasa yazo da shirinshi,a 6oye ya fara yin bincikenshi ba tare da kowa ya sani ba,ana haka kuma Mommynsu ta kirashi ta sanar dashi game da makudan kudin dasu twins suka bukata awurinta,ta tabbatar mashi akwae abunda yake faruwa dasu wanda suka 6oye don a yadda suka bukaci kudin sam hankalinsu ba'a kwance yake ba,gashi itama ta bukaci sai sun shirya tsakaninta da Junaid wanda tana ganin hakan ba mai yuwuwa bane cikin sauki,amman sai gashi sun aikata hakan duk don ta basu kudin,hakan yasa mata zarginsu,jin hakan yasa Sgr yin amfani da Surveillance Cameras wadanda yasa a wasu bangarori na gidan ba tare da kowa ya sani ba don bai barsu a bayyane ba wasu har a cikin chandeliers(fitilun sama) na parlon gidan aka sa,ta nan yake ganin duk abunda ke faruwa har lokacin dasu twins din suka kaima haroon kudin wanda daga baya yabi ya daukesu,koda ace asirin Azmee bai tonu ba ta hanyar ya Mu'allim ba,Sgr na gab da ganota,atakaice ma kusan ya gane bata da gaskia shiyasa ko lokacin da Abu ta sanar dashi dalilin ciwon Sehrish da kuma inda tasan Azmee yayi murmushin takaici,haka lokacin da Marshal Omar ke lallaba haroon akan ya sanar dasu wanda ke bashi umarni yace Sgr yasan komae,wannan kenan.


Azmee taci gaba da bayani "Tunkafin Afkuwar wannan Lamarin,Akwai sihiri ajikin Junaid,Wanda mukayi mashi turenshi,a duk daren duniya,dunƙulen jini na fita daga hancinshi batare da sanin kowa ba,Saboda bai sanar daku ba,bayan Faruwar Accident ɗin nan ni nasa aka killace mun Junaid,kuma na hana kowa Ya cutar mun dashi,Lokacin da kuka sanar cewa Junaid Anyi kidnapping dinshi,Nayi mamaki sosai,Yarda kuka tsara hakan bayan a iya saninku mutuwa Yayi,Sai kuma nayi tunanin cewa Kun 6oye mutuwar Junaid ne saboda mahaifinku gudun kada ku rasa shi,bakowa ya fara Zargina ba,Sae Sehrish da ta tsinci zoben Junaid a cikin wardrobe ɗina,tundaga nan ta fara sanya mun ido,ni kuma nayi kokarin rikitar da ita har ta fara ƴan gane gane..............."


Tunkan takai ƙarshen Maganar,Omar ya katse ta da cewa"Yanzu ina Junaid Yake,"?yayi tambayar tamkar baisan inda yake ba,

Shuru Azmee Ta ɗanyi kafin tace"daga bayan nan Nasa an kaishi gidan Hajiya saratu,Ɗiyar wan mahaifina wadda ke acikin garin nan,"..

  "Innalallahi wa'inna ilahirraji'un!!" Amrish ce ta ambaci hakan tare da ɗaura hannunta asaman kanta,Tana kuka,

Hankalin kowa Ya koma kanta,Muryarta na kerma ta nuna Azmee da hannunta tana faɗin"Dama ke kikasa aka kaishi gidanmu dan baƙin zalunci?Wacece ke?Ni bansan meya haɗani da ku ba,Wlh duk na tsani kaina,In har abunda nake zargi ya tabbata,wlh saina kashe kaina,"sosai ta fashe da kuka 


Tunda Azmee taji hakan nan ta gane cewa wani abu ya faru acan gidan,tabbas Junaid Ya ku6uta daga wurinsu,.

Gyaran murya Ya Mu'allim yayi,hankalinsu ya dawo kanshi,Anan Yake labarta masu duk abunda ya faru kamar yarda Amrish ta sanar dashi,Har zuwa kaishi asibiti da su kayi,


Yana kai ƙarshen maganar,Azeemi tace"Naji daɗi da Junaid ya dawo hannunku,Amrish ke bakowa bace face ɗiyar saratu matar ƙanina Ya Sayyadi,Da saratu dani ƴa'ƴan wa da kanine,Don haka ke jininmu ce gaba da baya,babu yarda zakiyi haka Allah Ya ƙaddaro maki,Ki gode ma Allah da baki ɗaukko irin mugayen ɗabi'un mahaifinki da mahaifiyarki ba wanda hakan ne ma yasa ba'a bayyana maki mahaifin naki ba,"


Waro ido waje Amrish tayi,idanuwanta sunyi jawur dasu,a fujajan ta watsa da gudu ta nufi Glass cups ɗin da suka faffashe a wurin,ta ɗauko ta daddage zata Caka shi a ƙahon zuciyarta da sauri Kanal Yusuf yayi hanzarin damƙar hannunta,ƙoƙarin kwacewa tadinga yi don ta Caka ma kanta,Amma ya hana hakan,Fisge glass ɗin yayi tare da jefar dashi ƙasa,Ya ruko kafaɗunta ya jinjigata"baki da hankali ne?Saboda me zaki kashe kanki?saboda Iyayenki sun kasance Gur6atattu!Laifinki ne?ko kin manta da ayar da Allah subhanahu wata Allah ke cewa"Yana fitar da mai rai daga matacce kuma yana fitar da matacce daga mai rai,kuma yana rayar da ƙasa a bayan mutuwarta,Kuma haka ake fitar daku,acikin suratul rum Ayata 20,Bayan ita akwai surar da tayi magana makamancin wannan acikin suratul Ahli'emran Aya ta 28,don haka ki kwantar da hankalinki,Ki rungumi ƙaddararki,Bakanki farau ba,Sau nawa cikakken malami ke haihuwar 6arawo ko kasurgumin dan fashi?Ba yadda Allah bai ikonshi,kuma bawai don baya sonku ba face don Ya jaraba imaninku,Sannan Laifin da iyayenki suka aikata bazai ta6a shafarki ba,ki gode ma Allah da baki ɗauko irin ɗabi'unsu ba,Ke tsarkakkiyace,Allah ya tsarkake ki daga faɗawa halaka.......'jikinta ba ƙaramin Sanyi yayi ba,Kalaman kanal Yusuf ba ƙaramin sanyaya mata zuciyarta su kayi ba,Har taji ta haƙura da kashe kanta da tace zata yi,Jiki asanyaye ta juya ta koma wurin Sehrish,rungumeta Sehrish tayi ajikinta,gaba ɗaya suka fashe da kuka maicin rai,dole Amrish taji ba daɗi,very heart touching ace iyayenka su dukansu gur6atattune kuma 6atattu,dayawa mutane zasu dinga yi maka wani mummunan kallo,Ya Allah kasa mu dace,



"Nasan bazaku ta6a yafe mun ba,Ku yanke mun duk hukuncin da ya dace dani,wlh zan kar6eshi hannu bibbiyu,Amma dan Allah ina neman wata alfarma ɗaya agare ku,"Azmee ce tayi maganar,yayin da kwalla ke cigaba da zubowa akan fuskarta,


Kasa kunne su kayi suna sauraronta,

"Dan Allah,Kada ku ta6a Haroon,Duk hukuncin da zaku yi mashi,Ni kuyi mun saboda ba laifin shi bane,tursasa mashi akayi,Bayan tafiyarku asibiti,Na same shi acikin mawuyacin hali ɗakin da kuka kwantar dashi,Na kwanceshi sannan na fitar dashi daga cikin gidan nan,Saboda gudun kada ku kashe shi nasan bazaku ƙyaleshi ba"


"Azmee kin bani mamaki,Kin karya mana zuciyoyinmu,Bakisan irin raɗaɗin da kika sanya mana acikin Zuciyoyinmu ba,Why Azmee?Duk don saboda daukar fansa Yasa kika shiga jikinmu!Ina iliminki ya tafi ne?Ke fa musulmace,bakiyi imani da ƙaddara bane?Meyasa Laifin wani zai shafe mu ?ballantana ma Ba wani abu akayi maku ba,Komai ya faru da family dinku laifinku ne,Saboda kun kashe ne shiyasa aka kashe naku,Da baku ta6a kowa ba,babu wanda zai ta6a naku,Kuskure ɗayane na kashe mijinki da akayi wanda shima don ya taka sahun 6arawo ne,Tsautsayine ya rutsa dashi....."daƙyar yake magana,sauke ajiyar zuciya yayi kafin yaci gaba da cewa"Almost 20 years Azmee kina tare damu ashe ba don Allah bane,Wlh tausayinki nake ji,Kin 6ata wayonki,kuma kinyi asarar Rayuwarki,Yanzu komai da kikayi ya tashi abanza,hatta ibadar da kikeyi itama ta tashi abanza,Idan yanzu kika faɗi kika mutu me zaki ce ma Allah?ya ƙarasa maganar yana kallonta,Sosai Azmee ta fashe da kuka kamar ranta zai fita 

  "Da ace kinyi hakuri,kin rungumi ƙaddara,Yaya kike tunanin Rayuwarki zata kasance?yadda kowa ke sonki,Kina da farin jini sosai,Ko abokanaina in suka zo gidan nan har santin girkinki suke yi,Kowa yabonki yake yi,Why Azmee?Kin ɗauki alhakin mutane dayawa,Kin cuce mu kin yaudare mu,kin kuma zalunce mu,Amma inaso ki sani,Wlh duk kanki kikayi mawa!"abun ya ƙona mashi rai sosai,

  "Ni wlh da tun farko kin sanar dani cewa kina sona,a yadda na yaba da kyawun halayanki a wannan lokacin,Da ba abunda zai hana in aure ki!"

  Ɗagowa tayi da idanuwanta waɗanda su kayi jawur dasu,tana kallon Abba dake magana,

 Rai a6ace Mommy tace"Ni bansan me kuke jira da ita ba,Banason ganin matar nan,Rayuwarta bata da amfani,ta mutu kowa ya huta,"


Gaba daya sun fusata,ganin suna ƙokarin zame belt ɗin wandonsu don su jibgeta,Abba yayi saurin dakatar dasu"Innallaha ma'assabirin!Kubarta da Allah Shiyasan yarda zaiyi da ita,ban amince ɗaya daga cikinku Ya ta6a lafiyar jikinta ba,Azmee bata kashe mun kowa ba,Iya cuta dai ta cutar damu,Ina neman alfarma a wurinku,daku miƙata wurin hukuma su yanke mata hukuncin daya dace da ita,Sannan kuma Ina umartarku da ku hanzarta Ruguza ƙungiyarsu,Da duk wani wanda ke cikinta,Kamar yarda kakanku salahudeen yayi,haka nakeso kuma Kuyi,Kada ku raga masu,banaso daya daga cikinsu Yasha,gawawwakinsu kawai nakeson Gani,"Yana kai ƙarshen maganar,Ya juya tare da barin wurin Ya koma bedroom ɗinshi,Idanuwanshi cike tab da kwalla,a ƙopar ɗakin ya tsaya yayin da idonshi ke akan Junaid dake kwance saman gadonshi Yana ta sharar bacci abunshi,Har cikin ranshi baiso Azmee Ta kasance haka ba,Koma miye ita taja ma kanta,Ya Allah kakare mu daga aikata Aikin dana Sani,


Bayan tafiyar Abba,Ya Mu'allim Yace"Shawarar da zan baku shine,Kuyi amfani da Azmee wurin kama sauran masu aikata laifin,saboda tasan komai,Tasan inda ƙungiyarsu take Inyaso daga bisani Sai a miƙata ga hukuma,zamu tayaku da Addu'a akan Allah ya baku nasara,"


Sosai sukayi ma Ya mu'allim Godiya,domin kuwa ya basu shawara mai kyau kuma Ya taimakesu,batare da 6ata Lokaci ba,suka tasa ƙeyar Azmee zuwa Ɗakin horonsu,Tambayoyi suka shiga jero mata,tana amsa masu,In tayi kuskuren yi masu taurin kai kuwa,zazzafan Mari take sha,Anan suka samu bayanin inda Ya sayyadi Yake,Ashe baya ƙasar tun Lokacin da abu ta kashe mashi idanuwanshi,Suka fiddashi ƙasar waje,Don a duba lafiyarshi,Da wayar Azmee sukayi amfani wurin gano Duk wani mugun abu da suke aikatawa,A ranar suka shirya tsaf cikin kakin Sojojinsu gaba dayansu domin fara yaƙar ƙungiyarsu,Manya manyan makamai suka ɗauka,Sai da Abba ya fara sanya masu Albarka,Yayi masu addu'a,Mommy ma tayi masu tare da sauran Mutanan gidan Kafin Su kayi masu sallama,A tare da Azmee suka tafi Asaman Helicopter kusan guda shida Ya ɗaga dasu,


Kasa samun natsuwa su Sehrish su kayi,kowa zullumin yake yi game da tafiyarsu Babban Yaya,wurine mai matukar haɗarin gaske acikin wani ƙurmamin daji,inda suka kafa ƙungiyarsu ta matsafa,kodai su kashe ko akashe su,Allah kaɗai yasan wanda zaiyi nasara,


Abu kamar wasa har goma sha ɗayan dare basu dawo ba,babu wani labari dangane dasu,Wayoyinsu kuma duk in aka kira bata shiga,Hakan Ya ƙara tayar masu da hankalinsu,shi kanshi Abba sai daga baya ya fara danasanin turasu,Mommy kuwa tuni ta fara zubda kwalla,tsoranta kada ta rasa Ƴa'ƴanta,

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

A 6angaren su Sehrish kuwa,Babu wanda ya runtsa acikinsu,kwana su kayi saman darduma sunayin sallah akan Allah ya basu nasara ya kuma dawo dasu Lafiya,abu kamar wasa Tsawon kwana biyu kenan su Sgr basu dawo ba,lamarin ya fara tsoratar dasu,Gashi ba'a samun Layinsu balle asan awani hali suke Ciki,


Sai adaren Rana ta biyu ne,Allah yayi suka dawo,Sunyi nasara sai dai sunyi babban rashi na mutun ɗaya acikinsu,Irfan Allah yayi mashi rasuwa,sunji mutuwar nan kamar kamar me,tare da gawarshi suka dawo,wasu daga cikinsu kuma sun raunata sosai,Dan Fawan Allah ne yayi zai rayu,Twins kuwa sun jigata sosai,kowa Yaji ajikinshi,Nasarorin da suka samu sune sun ruguza Ƙungiyar matsafan,sun lalata masu komai,Sun kuma kashe mutanan cikinta gaba ɗayansu,don sunyi masu zuwan bazata,kuma sunci sa'a adai dai lokacin suna kan yin meeting ne,kowa Ya hallara,Hada shugaban nasu Ghali,Da taimakon Azmee suka kashe shi,Yanzu mutun ɗaya ya rage masu su kamashi Wato Ya Sayyadi,



A washe garin ranar akayi jana'izar Irfan,Abba Yafi kowa jin mutuwar nan,Abubuwa sunyi mashi yawa,Ga Junaid dake kwance yana jinya,Ga kuma fawan shima Yana ƙarkashin kulawar likitoci,


Bayan kammala Jana'izar Ifran,Batare da 6ata Lokaci ba,Sgr Ya tura Armstrong tare da wasu daga cikin sojojinshi,Suka hau jirgi zuwa ƙasar Malaysia,Don bala'e har asibitin da aka kwantar da Ya sayyadi suka Cafko shi,idanuwanshi Na manne da uban bandegi,da Alama aiki akayi mashi a wurin,Cikin jirgi suka sanyoshi,Sannan Suka dawo dashi Nigeria,har cikin gidan suka taso ƙeyarshi gaba,a garden ɗin gidan Sgr ya sanyasu suka Kwantar mashi dashi,kafin ya yanke mashi hukunci,Sai da Ya fara kiran Abusufyan tare dasu Jahad,da oummansu gaba ɗayansu suka hallara a garden ɗin,

Abusufyan yace"dama saida na faɗa maka,Wannan ranar zata zo,kuma gata Allah ya nuna mun da raina da lafiyata,Gani ga kuma Yaran daka zalunta,Ga kuma mahaifiyarsu,Kaji haushin rayuwarka Sayyad,A yau ƙarshenka yazo,tun a gidan duniya zaka fara ɗanɗani raɗaɗin azaba,kafin ka koma Ga Allah," gaba ɗaya yabi ya ruɗe,jikinshi sai kerma Yake yi,daga yayi ƙoƙarin buɗe baki zai basu haƙuri,Sai Sgr ya Kai mashi naushi a kuncinshi,duk saida Ya zubar mashi da haƙoran bakinshi,Jini jaga jaga A bakinshi,

 "Mugu azzalumi,Ni Ko kaɗan banji tausayinka ba,Allah yaji ƙanka don nasan cewa taka ta ƙare,Allah ya ƙara nauyin ƙasa,"Abuce tayi maganar,

  Jahad da sehrish basu ce komai ba,Hosana dai ce Ta tofa mashi Miyau Asaman fuskarshi,bayan sun gama gaya mashi magana,Sgr Yaba sehrish umarnin ta kawo mashi tafasasshen Mai,


Jiki na rawa ta juya ta koma cikin gidan,Oummansu dasu Jahad suka bi bayanta,Bada jimawa ba ta dawo hannunta ɗauke da ƙaramar tukunya,Tafasasshen mai ne aciki sai tartsatsi yake yi,

  Umarni yaba Su armstrong,Su cire wandon jikinshi,Ganin haka yasa Sehrish ta ajiye man,ta watsa da gudu ta koma cikin gida gabanta na faɗuwa,

  Bayan sun cire wandonshi,suka yi mashi zirr,sojoji guda biyu suka tale ƙafafunshi,Abun nan da yake takama dashi yana yi ma mutane iskanci dashi,Sgr ya ɗauki tafasasshen man nan ya kwarara mashi agabanshi gaba ɗaya,

 Wa'iyazubillahi!Wata irin kururuwa Ya sayyadi yayi,lokacin da gabanshi ke ƙonewa,wani irin raɗaɗin azaba Ya dinga ji,Gaba ɗaya ya zauce ya gigice Ya fita hayyacinshi,


Umarni Ya basu Su ɗauke shi su kaishi can cikin ƙurmin daji,ko namun dawa sun samu abinci,A ƙarshe dae Ya sayyadi A cikin daji rayuwarshi ta ƙare,gawarshi A wulaƙance A ƙasƙance abun ba kyan gani,



Ita kuma Azmee Tare da Saratu,Jami'an ƴan sanda ne suka tafi dasu,Bayan an tattara hujjoji,Suka miƙasu Court domin Yin shari'a,A ƙarshe Aka yanke masu hukuncin zama gidan Yari,A ɗakin duhu na tsawon shekara 20,Sehrish tasha kuka,Saboda har lokacin tana son Azmee,Lokacin da aka kammala shari'ar za'a tafi dasu gidan Yari,Daƙyar aka rabasu,Sun rungume juna sosai suna kuka,ita da Sehrish,ita kam Amrish kin zuwa tayi wurin Mommynta balle ma ta rungumetan dama dakyar ta biyo su kotun,kowa baiji daɗin halin da Azmee ta jefa kanta ba,ba lalle ne lokacin da zasu fito ɗakin duhu ba,su dawo da idanuwansu ba,zaiyi wuya in basu makance ba,idan ma sun rayu kenan,'



Lokacin da Labarin mutuwar Irfan ta riski danginsu,Lokaci bai cika kwana biyu da rasuwa ba,Gidan Ya cika fam da masu zuwa yi masu jajen abunda Ya faru,Da kuma Yi masu gaisuwar rashin da suka yi,Mutane dayawa Sunyi mamakin jin cewa Azmee ce take ɗaukar fansa akan mutanan gidan,Sunyi Allah wadai da halinta,Tasha Zagi wurin jama'a don wasu da suna da halin da zasu ganta sai sun kasheta da bugu,Yanzu Alhamdulillah basu da wata sauran fargaba,NO MORE TENSION,


   Kowa yayi dakyau don kanshi,


*Boss Bature*


Wuraren ƙarfe 6 na marece,A jere motoci suka dinga shararowa izuwa cikin gidan,dankara dankaran gaske,Bayan sunyi parking ɗin motocin,Mota ta farko,Wani sergent Ya fito tare da zagaya Ya buɗe gidan baya,A hankali ta sauko daga cikin motar,jikinta sanye da code lace fari,Bakowa bace face Hajiya Azeema,fuskarta ɗauke da murmushi,other side ɗin hafsat ce ta fito jikinta sanye da atampa,Ta ruƙo hand bag dinta,

  Motar bayansu,Ammi ce tare da Gwaggon katsina,Dr harriss ne yayi driving dinsu,Saude na a gefenshi,

Daga Motarsu kuma sai Motar MG Osman,Tare da Captain adam,basu kaɗai bane a motar,Akwai Ƴan matan da suka zo dasu kyawawan gaske daga Gani ƴan uwansu ne,

  Motar dake bayansu Motar Captain Najeeb ce,su biyu ne aciki shi da Talal autansu na biyu,


Babu wanda yasan a ranar zasu dawo,


A lokacin gaba ɗayansu sun hallara asaman dining suna Cin dinner ɗinsu,banda mutun biyu Omar da Sgr basu kaiga dawowa daga wurin aiki ba,They're busy for work ga prepation ɗin da suke yi Na Komawa U.S tafiya ta kankama,kowa ka kalli fuskarshi daurewa kawai suke yi akwai sauran jimami,Yanzu babu Azmee sai dai Abu dasu Jahad ke girka abincin gidan,



Sehrish ta zabga uban tagumi,Bakowa take tunani ba,face Aunty azmee,Duk in oummansu Nayi serving ɗinsu abinci,Sai ta dinga tunawa da ita,


Binsu da kallo ta soma yi ɗaya bayan ɗaya,tun daga kan mommy dake ta faman jujjuya cokali acikin abincin gabanta,Abba kuwa tunda ya zauna Bai ta6a komai ba,Lemu kawai yake tasha,

Su twins Da ɗan dama,Sun saki jikinsu suna cin abinci,Haka kanal yusif ma sosai yake Cin abincinshi,Irfan da jabeer still sai a hankali,Duk sun kasa sakewa saboda rashin Irfan da su kayi acikinsu,


Kallon Hosana tayi,Cinyar kaza ta ɗauko ta tura abakinta sai tauna take yi kamar akuya ta samu ciyawa,Murmushi sehrish ta ɗanyi tare da ɗan girgiza kanta,Mayar da idanuwanta tayi kan Amrish dake zaune daƙyar take tura abinci abakinta har yau ta kasa sakewa acikinsu,ɗagowa tayi suka haɗa ido Da sehrish atare suka sakarwa Juna murmushi,


  Miƙewa Jahad tayi,"Where are u going"?Abusufyan ne ya tambayeta ganin ta miƙe tsaye bata kammala cin abincin ba,

  Sunnar dakai ta ɗanyi kafin tace"Zanje na duba jikin junaid ne"

Murmushi ya saki,kafin yace"Je ki abunki,Allah yabar ƙauna,"


Kunyace ta rufe ta,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta,da sauri tabar wurin ta nufi bedroom ɗin abba,


Bayan tafiyar Jahad mommy ta mike"Zanje na duba jikin fawan,Inaso naji idan akwai abunda yake buƙata sai in kai mashi,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kama hanyar bedroom ɗinshi,

Lokacin da jahad ta ƙarasa bedroom ɗin a ƙopar ɗakin ta tsaya,tare da sanya hannu ta ruke handle ɗin ƙopar,Slowly ta tura ƙopar ɗakin ta ɗan leƙa,har yanzu bawan Allah a kwance yake baisan inda kanshi yake ba,Da alama Ya samu bacci,kullum sai Ya mu'allim yazo duba shi,yanzu ya zama tamkar ɗan uwa agaresu,


A hankali take tafiya harta ƙarasa gefen gadon ta zauna,Zuba mashi ido tayi tana kallonshi,Yanzu bata da burin daya wuce taga junaid Ya dawo cikin hayyacinshi,Fargabarta kada Ya manta da soyayyarsu,


A hankali ta kwantar da kanta gefenshi,Allah ya baka Lafiya My Romeo,ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta,Unexpect Taji Saukar hannunshi acikin Sumar kanta,A firgice ta ɗago da kanta tana kallon fuskarshi,slowly ya buɗe dara daran idanuwanshi farare ƙyal akan fuskarta,La66anta na kerma Ta ambaci Sunanshi JUNAID! da mamaki akan fuskarta,Binta da ido yayi yana kallonta,Matsawa tayi saitin fuskarshi,

  Cike da tsantsar farin ciki ta kuma ambaton sunanshi"Junaid"

  Lumshe mata idanuwanshi yayi tare da sake budesu akan fuskarta,Saboda tsabar farin Ciki,Da sauri ta sauko daga saman gadon ta watsa da gudu ta fito daga ɗakin,Jin takun takalmata yajanyo hankalinsu akanta,

  Tunkafin ta isa ta soma magana"Abba Junaid ya farka,Ya dawo cikin hayyacinshi,"Gaba ɗaya suka miƙe Fuskar kowannansu ɗauke da tsantsar farin Ciki suke kallonta,Adai dai Lokacin Gwaggon Katsina Ta dako masu Sallama da ƙarfin gaske tana fadin"Gafara dai,Mai wuri yazo Me tabarma ya naɗe,Masu Gidan sun dawo,"



>>>Also Click Here To Download Complete Book Document


*Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*

 

 Click Here To Download This Book



Latsa Nan Domin Sauke Wannan Littafin A Wayarka

Comments