MAHAUKACI NE KO ALJANI? 🧟♂️
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Mallakin
Aisha Abdullahi Yabo
*بسم الله الر حمن الر حيم*
___________________________________
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
3&4
Kusanto ta da ya ke hakan ya sa numfashin ta ya din ɗauke wa sannu a hankali ta rufe idanu za ta ƙwalla ihu kawai ta farka da ga nannauyan baccin da ta ke. Zama ta yi a tsakiyar gado zuciyar ta na halbawa da sauri da sauri "waye wannan ne da ya ke zuwa mini cikin bacci? MAHAUKACI NE KO ALJANI?" Ta yi wa kan ta tambayar da ba ta da mai amsa ma ta. Lalubo wayarta ta yi da ta ke ƙasan filo ta duba agogo ƙarfe biyun dare koma wa ta yi ta kwanta ta takure waje ɗaya idanunta a lumshi tsoro ne fal a zuciyarta ji ta ke kamar ta je ta tashi su Dady sai dai kuma haka ta danni abin har wani sabon baccin ya zo ya yi awon gaba da ita.
Zaune ta ke a cikin aji Nabila ta shigo ta zauna a kusa da ita "Mina lafiya ki ke kuwa? Kowa ya fita sai ke kaɗai kin buga uban tagumi" janye tagumin ta yi ta na kallon Nabila "ba komai kawai yau hayaniyar ce ba na so" ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta na ɗaukar jakarta ta ce. "Gida ma zan tafi"
"Kai kin sa ni mu na da lecture ƙarfe huɗu shi ne kuma za ki tafi, ki na sa ni da halin malamin nan ba ya da mutunci ko?"
"Mtsw! Ba abin da ya isa ya yi mini, karatun na shi ne ban yi niyar yi ba ba kuma zan tsaya ba ya yi duk abin da zai yi" ta bi ta gefen ta ta wuce Nabila ta ɗaga kafaɗar "ai shi kenan a sauka lafiya" a harabar makarantar ta haɗu da su TK "Babbar yarinya ya na ganki kin yi wani sanyi da yawa ko ba ki da lafiya ne?" Lumshi idanunta ta yi komai ba ta ce da shi ba ta ɗan yi gaba "lau na ke kawai na ga ji da zaman makarantar ne" ta bashi amsa ba tare da ta juyo ba ta yi gaba abin ta, tafiya ya yi da sauri ya shiga gabanta ya na faɗin "haba Mina yanzu saura minti goma fa mu shiga lecture kuma shi ne za ki yi tafiyar ki. Please ki b...
Ɗa ga masa hannu ta yi "na ce ba zan tsaya ba dole ne?" Ta ɗan yi tsaki tare da barin wajan
Hannu yasa a cikin aljihun wandon shi ya bi bayanta da kallo "TK ka na janyo mana raini a wajan yarinyar nan wallahi da ba dan kai ba da ba abin da zai sa na din ga shiga sabgar ta. Yarinya sai shigen izza"
"Nasir kun kasa fahimtar ta ne tabbas ta na da izza da jiji da kai amma idan ka fahimci zahirin rayuwar ta ta na da wasu kwalitin da za a so mu'amala da ita"
"Humm dama ai za ka faɗi hakan, Hausawa su kan ce so hana ganin laifi, sai dai ina jiye ma ka faɗawa komar wulaƙancin ta duk ranar da ka faɗa ma ta gaskiyar abin da ya ke zuciyar ka" cewar Fa'iz. Dariya ya yi irin na wanda ya yarda da kan shi ya na faɗin "sai dai idan ban faɗa ma ta ba, ina da tabbacin da ga ranar da na faɗa mata sirrin zuciyata da ga ranar za ta kware wa soyayya ta, ko shakka ba na yi"
"Hahaha shi ya sa ai na ga har yanzu ka kasa faɗa ma ta sai bulayi ka ke ba"
"Wai hakan ku ke gani? To ku kwantar da hankalin ku a cikin satin nan kuwa zan faɗa ma ta kuma za ku tabbatar da zance na gaskiya ne"
"Ai shi kenan ga mu ga ni" cewar Nasir. Saurin barin wajan su ka yi su ka nufi aji ganin malami na tahuwa, sauran ɗalibai a ka nufi aji.
A ƙofar shiga babban falon su ka yi karo da juna har kansu ya garu riƙi kanta ta yi dan wani irin azabar ciwo da ta ji. Inna Hansa'u mai masu girki ta durƙushe a wajan cikin tsoro da tashin hankali ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri wallahi ban san za ki shi go ba" wani irin kallo ta watsa mata "ki yi haƙuri don Allah"
"Uhm! Tasu" Mina ta yi maganar ta na mai yi ma ta ƙuru da idanu. Jiki na rawa ta miƙe tsaye ta buɗe baki ta yi magana ta wanka ma ta mari a fuska hakan ya tilasta ta yin shiru tare da sakin baki ta na kallon zafin marin da mamaki su ka hade ma ta a tare, duk rashin mutuncin da Mina ta ke ma su ko da wasa ba ta taɓa tsamanin za ta iya ɗa ga hannu ta mare ta ba. "Gobe ma sai ki ƙara sakarya kawai!"
"Mene ne haka Mina?" Momy ta yi tambayar ta na saukowa da ga matattakalar bene. Gefen Momy ta bi ta wuce ba tare da ko kallonta ta yi ba bare har ta ba ta amsa, bin ta da kallo Momy ta yi ta na gyaɗa kai ta juya ta kalle Inna Hansa'u da har yanzu ta ke da fi da kwance "Me ya faru ne?"
"Uhm! Hajiya na zo zan fita ne ban san da ita ba shi ne mu ka yi kaura, na ba ta haƙuri duk da hakan sai da ta mare ni"
Riƙi kanta ta yi cikin damuwa "Innalillahi mari kuma? Oh Allah ka shirya mini Amina. Don Allah Inna ki yi haƙuri wallahi halin Amina sai haƙuri, ku din ga kiyaye shiga sabgarta dan a tsira da mutunci tun da ita ɗin wata irin murɗaɗin hali ne da ita" murmushin takaici ta yi "ba komai Hajiya" ta juya jiki a sanyaye ta fita dan karɓo kayan wankin da Momy ta tura ta ta yi a wajan mai wankin su. Haura wa sama ta yi ta samu ta na zaune a tsakiyar gado ranta a ɓaci ta na dafi da goshin ta. zama ta yi gefen gado
"Me ya sa ba kya jin magana koyaushe ina ƙoƙarin raba ki da wannan halin na rashin ɗa'a ga manya amma kamar ina cewa je ki yi. Inna fa za ta yi jika da ke shi ne dan rashin haƙuri za ki mari tsohuwar muta ne"
Kuka ta sa ta na faɗin "ita ce fa ta bugi ni kalle goshi na har ya yi lolo" ta ƙarasa maganar ta na nuna ma ta, ajiyar zuciya Momy ta yi "shi kenan kukan ya isa haka, da ga an fara magana sai kuka. Tashi ki ci abinci"
"Ni ba zan ci ba" ta yi maganar a shagwaɓi shafa kanta ta yi cikin lalllashi "haba Shalelen Dady ba na ce ki yi haƙuri ba, kawai ba na so ne a ce ki na yi masu rashin kunya bakin mutane ba kyau, shi ya sa ki ke ganin ina yawan yi ma ki maganar ki gyara. Yi haƙuri ta su mu tafi ki ci abinci kin ji ko?"
"Ki je zan zo" ta faɗa ta na gyara kwanciyarta. Tashi tsaye ta yi ta na faɗin "shi kenan. Kin dai yi sallah ko" gyaɗa kan ta ta yi. "Me ya sa, ki daina wasa da sallah yanzu hakan ma ko Azahar ba ki yi ba"
"Duk yanzu zan yi" girgiza kai kawai Momy ta yi ta fice. Kwanciyar ta ta yi sai wuraren biyar ta tashi ta ɗauro alwala ta yi sallolin ta sannan ta sauko ƙasa.
Da dare su na zaune falon Dady ta yi matashi da cinyoyinsa ta na chat ya na kallon labarai Momy na gefen shi ta na haɗa masa shaye "yaww Dady ba ka dai manta da zancen tafiya ta ba ko?"
"Ban manta ba shalele ba kin ce ku na yin hutu ba za ki tafi" tashi ta yi ta zauna ta na faɗin "ni cikin watan nan na ke so na tafi na ga ji da zaman Nageria"
"Karatun kuma fa ki yi ya da shi?"
Turo baki ta yi ta na kallon Dady fuska a marairaici kamar za ta yi kuka, riƙo hannun ta ya yi "ƙyale ta kar ki ɓata ranki yaushe ki ke so ki tafi?"
"Ranar mondy ta sama"
"An gama, za a shirya ma ki tafiya, wace ƙasar ma ce ki ke son zuwa?"
Ta ɗaga kanta sama alamar tunani ta haɗi babban yatsan ta da manuni sannan ta sake su ta na faɗin "yawwa Dady Germany da kuma India tare da ƙawaye na za mu tafi"
"Allah ya nuna ma na, yadda duk ki ke so hakan za a yi Shalelena" rungome shi ta yi ta manna ma sa kiss a goshi sannan ta tashi ta bar falon da gudu. Miƙa ma sa shayen ta yi ya karɓa ya fara sha, cikin damuwa ta kalle shi ta na faɗin "Alhaji ina jiye mana gaba fa a kan lamarin Amina"
"To sarkin meta me kuma a ka yi?"
"Humm tambaya ta ma ka ke ko. Yanzu fa ta na tsaka da karatu za ta bar ƙasar nan ta bar karatun ta haba don Allah"
"To mene ne a ciki ai yanzu mu na lokacin da ba sai ka yi karatu ne za ka tsira da takardun makaranta ba kuɗi su ne su ke yin komai. Tun da hakan ta ke so kin sa ni ba zan hana ta abin da ta ke so ba" gyaɗa kanta ta yi cikin nuna rashin jin daɗi ta ce. "Ya ka ma ta yarinyar nan ta san rayuwa ba komai ne a ke so a kuma samu ba, ita fa mace ce da za ta tafi gidan wani a ƙarƙashin wani za ta zauna dole ita ce za ta bi abin da ya ke so ba shi ne zai bi abin da ta ke so ba. Ka ga kuwa tun a gida ya kamata a ce ta tasu da wannan a ranta"
"Sai kuma a ka ce da ke zan aura ma ta miji wanda zai juya mini yarinya yadda ya so? Ita kaɗai fa na mallaka a duniyar nan ta ya kuwa ba zan faranta ma ta rai ba. Ban nemi komai na rasa a rayuwar nan ba, dan haka ita ma ba za ta taɓa nema ta rasa ba tun da Allah ya hure mini" shiru ta masa ta sa ni idan za su kwana su wuni ba zai taɓa fahimtar ta ba bare har ta sa ran da zai sauya ɗin. Hakan ya sa ta sauya zancen "Alhaji ɗazun Na'ima ta kira ni ta ke cewa na tuna ma ka zancen kuɗin da ta ce ka ba ta"
"Mtsw!! Na'ima yawan bani bani ɗin ta ya yi yawa koyaushe ba ta rabo da matsala"
"Haba dai ai dan ka na da ne har ta ke nema a wajan ka tun da wa ta ke da shi a duniyar nan da za ta nemi abu a wajan sa sama da kai, haƙuri za ka yi ka ba ta tun da Allah ya haɗa ta da Namiji mai matattar zuciya"
"Na ji zan bata ɗin"
"Yaushe?"
"A'a ba na ce zan bata ba, zan ba ta. Kawai ta zauna da miji marar zuciya nema sai ka ce shi ne autan maza ta barshi ta fito ta aure mijin ƙwarai mana ba wai mu na maza ba" dariya ta yi ta ma faɗin "ta na son mijin ta za ka ce ta fito ta bar shi, sannan kuma 'ya'ya biyar ai ba wasa ba ne, ta bar wa wa yaran. Ka dai yi haƙuri ka ba ta jarin ka haɗa har shi ɗin"
"Ita ɗin dai da ta ke dole na, amma shi sisin kwabo ba zan ba shi ba, idan zai tashi ya nema ya tashi ya nema kamar kowa"
"Humm to ai an gode tun da har za ka ba ta ɗin."
Zaune ya ke gindin wani gida mai kama da kango kasancewar ginin gidan ya fara rubtawa ga shi babu rufi a saman, hakan kuma babu ƙofa. A takure ya ke waje ɗaya ya sa kan shi a tsakankanin gwauwoyin shi har wayau dai gashin kan shi ya sauko kamar na mace. Zuba masa idanu ta yi a ranta ta na ji kamar ta je ta ga ainahin waye shi tun da dai yau kam ta gan shi a zahiri kuma babu guguwa ko dare bare har ta ji tsoron. Sai dai tsoro ya sa ta na ji kawai ta yi tafiyar ta. Har ta juya za ta nufi wajan da ta a jiye motar ta tsaya idanunta a lumshi zuciyarta azalzalarta ta ke da ta je wajan shi, ba tare da ta tsaya dogon tunani ba kawai ta nufi wajan shi zuciyarta na dukan uku-uku.
Durƙushewa ta yi a gaban shi cikin rawar murya ta ce. "Sannu" ɗago kan shi ya yi ya na kallon ta da idanun shi da su ke zubar da hawaye "me ya faru babba da kai ka ke kuka" shiru ya ma ta sai da ta sake maimaita tambayar "yunwa na ke ji" tuntsirewa ta yi da dariya har sai da ta kai ƙasa ta yi zaman 'yan buri bai ce da ita komai ba sai kallon ta da ya ke sai da ta yi mai isar ta kafin ta tsagaita da dariyar ta na faɗin "yanzu kai ƙato da kai ka ke kukan yunwa. Ok ina zuwa" tashi ta yi ta je mota ta ɗauko abu a cikin leda ta kawo ma shi ta na da ga tsaye ta miƙa masa
"Mene ne?" Ya yi ma ta tambayar ba tare da ya karɓa ba, zama ta yi gaban shi ta na faɗin "kai dai ka karɓa ba yunwa ka ce ka na ji ba" karɓa ya yi ya na buɗe ledar wani abu dogo mai tudu ya gani sai wata ruba mai faɗi da zurfi. "wannan ai ba abinci ba ne"
"Waye ya faɗa ma ka ba abinci ba ne? Ka fara ci kafin ka yanki hukunci" bai sake cewa da ita komai ba ya fara ci ta karɓi robar ta buɗe ma shi, sai da ya canye tas ya karɓi robar ya kafa a bakin shi "ga cokali fa" ko kallon ta bai yi ba ya shanye tas ya yi wurgi da robar ya na faɗin "wannan abincin da daɗi ya ke"
"Shawarma kenan, da kuma fura da a ka haɗa da yoghurt da kwakwa"
"Za ki din ga kawo mini kullum?"
"Ko godiya fa ba ka mini ba sai kawai na din ga kawo ma ka kullum ga 'yar ga aikin ka ba" tashi ya yi ba tare da ya ce da ita komai ba ya fara tafiya ta miƙe tsaye idanunta a kan shi "au ba za ka mini godiya ba ko. To shi kenan waye kai, ya sunan ka, ina ne gidan ku?" Cak ya tsaya da ga tafiyar da ya ke tare da juyowa ya zuba ma ta idanu "ka yi shiru"
"Ni ma ban san waye ni ba, ban kuma san a ina na ke ba. Ko za ki taimaka ki faɗa mini asalin wane ne ni?" Fito da idanu ta yi ta na kwallon shi da matuƙar mamaki a fuskarta kiran da ya shigo wayar ta ne ya katse ma ta mafarkin da ta ke. Tashi ta yi ta zauna a tsakiyar gado tare da rungume filo a wannan karon kam sam ba ta so tashi baccin nan ba bare har a yanke ma ta mafarki 'wane ne shi? Anya ba MAHAUKACI BA NE? Kai wannan ALJANI NE. Wai ni ce zan faɗa masa waye shi. Me ya sa ya ke yawan zo min a cikin bacci na ne.?' kiran wayar ne ya katse mata zancen zucin da ta ke tsaki ta yi tare da kai hannu ta ɗaga kiran
"Mene ne wai a ke ta damuna da kira?"
"Yi haƙuri dama mun ji ki shiru ne ga shi ƙarfe biyar ki ka ce za ki fito" riƙi kanta ta yi "oh TK sam na manta bacci ne ya ɗauke ni. Zan yi sallah idan na shirya zan fito ku jira ni a in da mu ka saba haɗuwa zan same ku a can"
"An gama babbar yarinya" tsinki kiran ta yi tare da saukowa ta shiga banɗaki.
Dab da za ta fita Momy ta fito kichen "ina kuma za ki tafi yanzu da yamma nan"
"Momy za mu fita da ƙawaye na ne"
"Fitar tun da ba dole ba ce a bari sai gobe mana, yanzu magarib ta kusa kuma na san halin ki sai ki kai dare kafin ki dawo" turo baki ta yi ta na faɗin "ni dai na tafi ai ba zan daɗi ba" ba ta jira jin me za ta ce ba ta sa kai ta fita. "Allah ka shirya mini Amina."
Ranar talata su na zaune a harabar makaranta sai fira su ke ta masu shiru, kwana biyu ba ta yi mafarkin ta ba, haka kawai ta ke son sake ganin shi. "Mutuniyar ka fa na rasa me ya ke damun ta kwana biyu duk da dai dama ba yawan magana ne da ita ba amma shirun na ta ya yi yawa"
"Ni ma tunanin da na ke kenan Nabila ko za ki tambayar ma na ita idan a kwai abin da ya ke damun ta" fito da idanu ta yi ta na faɗin "wa? Hum-um kun fi kusa TK ka dai tambaye ta ka ji" komai bai ce da ita ba ya tashi ya zauna kujerar da take zaune
"Waye ne ya ke taɓa mini ke ne kwana biyu sam ba na gani kan ki, ko akwai abin da ya ke damun ki ne?" Shiru ta masa kamar ba za ta amsa ma shi ba can koma ta ce. "Ni na ce ma ka ina da damuwa ne?"
"Yanayin ki ne dai ya nuna hakan"
"To ni ba abin da ya ke damuna" murmushi ya yi "hakan na ke son ji dama, kin san ba na so na gan ki cikin damuwa gaba ɗaya sai na rasa me ya ke yi mini daɗi" murmushi kawai ta yi ta miƙe ya ɗauki jakar ta "ina kuma za ki tafi?"
Tafiyar ta ta yi ba tare da ta ce da shi komai ba. Riƙo hannun shi ya ji an yi hakan yasa ya juyo Nasir ne "ka na nufin yau ɗin na ma ba za ka faɗa ma ta ba?"
"Mtsw ka na ganin fa ba ta cikin yanayi mai daɗi, ta ya zan tunkare ta da wannan maganar"
"Hahaha dama na faɗa ma ka Nasir TK cika baki ne kawai ya iya ba zai iya faɗa ma ta ba, matsoracin gaske ne" harararsa TK ya yi "zan kuwa tabbatar ma ka da ni ɗin ba matsoraci ba ne"
"Uhm-um TK kar fa ka biye wa su Fa'iz"
"Manta da su sai na tabbatar ma su da Mina yau sai ta kwayewa soyayya ta" ya yi maganar a zuciye. "I LOVE YOU MINA TURAKI!! Cak ta tsaya ba ta tafi ba ba ta kuma juyo ba. Dukan hankalin 'yan mata da samarin da su ke wajan ya yo kan su.
Fulani