ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 5

🧟‍♀️🧟‍♀️                        🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/ft23GhvuEqc

*^ Part 5 ^*


Jan langar tayi gabanta ta bude taliyace dahuwar manja sai kamshin daddawa ke tashi, nan take ta fara aikawa cikinta dama yunwa take ji rabonta da abinci tun awara da waina da suka ci da safe. Lomar karshe da zata kai suka ji ana turo kyare "Wane munafurcin ne yasa aka rufe daki harda sa kuba dudu yaushe daren yayi". Laure ce ke magana Fatsuma da ta aika sauran lomar taliyar baki ta cewa Mairo ta bude kofar. Tana budewa Laure ta saki salati hade da kiran Kubura, da gudu Kubura ta taso tana fadin "Lafiya kuwa? Ko wani mugun abun suke aikatawa kamar yanda kika fada?". 


"Mugun abu ne mana yaya kinji yadda kamshin daddawa yake tashi a dakin mu muna can muna musu dariya zasu kwana da yunwa ashe yan iska suka daukemu". Kubura ta karaso hade da kutsawa cikin dakin, kai tsaye ta dauke langar taliyan dake gaban Fatsuma ta fara lashewa "Na rantse da Allah taliya, ce kinji dadin kuwa!". "Muji" Laure ta kai hannu ta lashi kwanon ta kai baki "Wallahi kuwa shegen dadi ta sha daddawa". zata kara kai hannu Kubura ta hana dan dole ta hakura tana lasar baki, sai da Kubura ta lashe kwanon tass harda sa harshe sannan ta juyo kan Fatsuma "Munafuka ido ciki-ciki ashe kallon yan iska kike mana kina da hanyar da zaki rika samun abincin fada mun wannan taliyar daga gidan ubanwa". 


Cikin sanyayyar muryarta tace "Yi hakuri Yaya nima bansan da ita ba Habiba Maman Salame ce ta ba Mairo ta kawo min". Ta dallawa Mairo da tayi tsuru tana kallonta harara dake yar fitilar joni dake rataye a dakin ta haske ko'ina "Munafuka ashe wucewar da kikayi sadaf-sadaf cikin hijabi dauke kike da abincin bamu lura ba to daga yau sai mun rika cajeki muna fuka mai bak'in hali". Mairo bata ce kala ba ta kauda kai don ko da tayi niyar yin magana mamanta zata tsawatar mata da cewa ba'a yiwa manya rashin kunya. Nan dai su Laure suka gama masifarsu hade da fadin maganganun da suka ga dama sannan suka bar dakin suna lasar harshe kamar mayu. A daren Mairo ta wanke kwanon ta kaiwa Mamasu Salame bayan sun gama wasunsu a dandali sannan ta dawo gida ta tarar da Ummanta tuni har tayi bacci itama ta kwanta gefenta ba dadewa bacci yayi gaba da ita


***************      ******      "***********

Daji ne mai cike da sarkakiya, wasu manya kuma dogayen bishiyoyi sun cike dajin ta ko ina ka waiga su kake ganin, abinda zai baka mamaki shine ko ka daga kai ba zaka iya hango karshen ko wace bishiya ba sai dai ka rika hangen rassanta. Kasantuwar hakan ya haifarwa dajin duhu ko da kuwa da tsakar rana ne. Sanye take da doguwar farar riga wacce duk ta kwaso yayi kafarta ba takalmi Allah kadai yasan iya kayoyin da ta taka amma hakan bai hanata gudu da take iya karbinta ba wanda ma iya kiransa da gudun fanfalaki musamman idan muka ga abinda ke binta baya.


Wasu irin halitti ne bakake su ba karnuka ba amma bakinsu yana kama da na karnuka sai dai ko kusa ba zaka kwatanta girmansu dana kare ba sun fi kare girma nesa ba kusa ba. Zankala-zankalan hakoransu a waje su wanda suka fito daga cikin katon bakin wanda ke zubar da jini shi kanshi bakin halittar zasu iya hadiye mutum ba tare da yayi tuntube a cikin bakin ba. Kafafunsu hudu ko wacce yatsa dauke da wasu irin farcina masu kaifin da kai kace wuka ce. Wannan halitu ne ke biye da Fatima dake falla gudu iya karfinta don ta tabbata idan suna kamata ko gawarta ba za'a tsinta ba


Ita dai ta kutsa kanta cikin wannan mugun daji amma bata san inda ta nufa ba. Gudu kawai take tana tsallake kananun itace da duwatsun da ke watse ko'ina a cikin dadin yayin da halittun ke biye da ita suna wani irin gunji wanda ya fi kama da na mayunwacin zaki. Ana cikin haka jijiyar wata bishiya ta sarke kafafun Fatima nan take ta fadi kasa kan kace kwabo tuni wannan halittu sun daka tsalle hade da kaiwa Fatima mummunan hari da nufin cinyeta. Sauran baifi taku biyu su karasa gareta ba sai gani sukayi wani haske ya bayyana cikin abinda baifi sekonni ba wata santaleliyar budurwa kyakyawa ta bayyana. Da ganinta Fatima tace "Safuratu" cikin jin dadi da ganinta


Ba tare da ta dubi Fatima ba ta dunkule hannu ta fara kaiwa wannan halittu naushi. Duk wanda ta nausa sai kaga yayi sama kwali ya tarwatse ya zama bakin hayaki. Haka ta cigaba da ragar-gazarsu ko kadan ta ki basu dama balle su samu damar taba jikinta ko jikin Fatima duk yawansu sai ya tashi a banza cikin lokaci kankani ta karar da su. Fatima ta tashi daga inda take cikin tsananin farin ciki ta nufi inda Safuratu take tsaye tana kallonta itama tana murmushi. Nan take suka ruga da nufin rungume juna saura baifi tako goma su karasa ga juna ba, ba zato ba tsamanin sai gani sukayi wani katon dodo marar kyan gani ya bayyana a gabansu nan take ya wangame baki ya dauki Safuratu da hannu daya yayi loma da ita ya hadiyeta.


Da faruwar hakan Fatima ta dora hannu a kai ta kwada uban ihu hade da fadin "Aljanata Safuratu... Wayyo! Aljanata!!" Firgigi Fatsuma ta farka da innalillahi a bakinta Mairo ta gani a gefanta na faman Fadin "Umma! Umma lafiya". Murje ido tayo hade da cewa "Lafiya kalau yaushe kika farka Baby?". "Umma ai ke kika tasheni da karfi kike ihu kina cewa aljanarki Safuratu wacece Safuratu ne naji kina yawon fadinta idan kina bacci". Shiru Fatsuma tayi sai kuma hawaye suka gangaro mata, shekaru da dama sun shude amma duk bayan kwana biyu zuwa uku sai tayi mafarki mai ban tsoro da hatsari game da ita kanta da aljanarta Safuratu abun yana matukar bata mamaki wanda hakan kuma na kara tabbatar mata tabbas ba abanza ba Safuratu tayi watsi da ita sai dai kuma ai ita aljana ce me zai sameta ta sha ji ance aljanu basa mutuwa da wuri.


Mairo ce ta katse mata tunanin da cewa "Umma ko yar uwarki ce wannan Safuratu din wacce ta mutu nasha tambayarki idan kikayi irin mafarkin nan amma sai dai inga kina kuka har yanzu baki fada min ko wacece ba". Hannu ta sa tama share hawaye a ranta take tunanin ko ya dace ta ba Mairo labarin Aljanarta Safuratu domin gani take Safuratu tayi karama babu abinda zata fahimta dangane da damuwarta. Amma kuma ta wani fannin maganganun Mairon suna bata mamaki in tayi wani furcin kamar babba. "Ba komai Baby tashi muyi sallah naji kamar kiran sallah ake idan munyi sallah zan fada miki ko wacece Safuratu". Da jin hakan dadi ya kume Mairo don tana son sanin wacece Safuratu ita bama wannan ba tasha jin mamarta na kiran Aljanata a cikin bacci..................

Comments