ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 19


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/LgVOwZek43U


http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-17-hausa.html


*^ Part 19 ^*



Tafe take ita da yarta mai kimanin shekara sha biyar, masifa take ba ji ba gani duk inda ta wuce kallonta ake a haka ta fado gidan tana kwalawa Fatsuma kira. Fatsuma na daki taji kiran. Hankalinta ba karamin tashi yayi ba lokacin da ta ji muryar Ladi ne, a zuciyarta ta ke tunanin me zata fadawa Ladi, domin kwakwalwarta tayi nauyi tun jiya take tunanin yadda zata bullowa lamarin amma har zuwa wannan lokaci bata iya tunano mafita ba, gashi yanzu har lokaci ya kore, dama ta san cewa ba makawa sai labari ya jewa Ladi. Amma da ta so ace ita taje mata da maganar. A sanyaye ta fito jiki ba kwari ta kalli Ladi tana sosa gefen wuya, "A'a Ladi kece a gidan shigo daga ciki mana". 


"Haba Fatsuma kin bani mamaki na rantse da Allah abinda kika aikata banji dadi ba, kinga Salbiya nan tun lokacin da ta fada min wannan labarin karyatata nayi a zatona ko a mafarki ba zaki aikata min haka ba, sai da na shigo gidan nan sannan na tabbatar da abinda ta fada min gaskiya ne domin ga shi a zahiri dai akuyata daya bata nan Fatsuma ina Akuyata?". 


Daburcewa Fatsuma tayi nan take tama rasa ta ina zata farawa Ladi bayani "Ina wuni Ladi ki shigo daga ciki mana, wallahi dama yanzu haka tunanin zuwa gidan naki nake". Hannu ta daga mata, "Kinga Fatsuma ba gaisuwa ce ta kawo ni gidanki ba. Zuwa nayi inji ina akuyata me ya faru da dukiyata shine kawai ya kawo ni, duk da naji ana ta maganar a gari amma na fi so inji daga bakinki daga nan kuma sai mu dora da bayanin yadda za'a fito min da akuyata". Gaban Fatsuma ne ya sake faduwa a karo na barkatai domin Allah ya gani bata san ta inda zata bullowa wannan lamari ba, don haka tayi shiru tana raraba idanu a tsakar gidan.


Kubura da Laure dake gefe suna kallo hade da murmushi irin na mugunta, Laure ta ce "Ke Fatsuma magana fa ake miki, ki fito fili ba wani boye-boye ki fada mata mijinki kika taimakawa baya da jari kika ce ya sayar da akuya yayi jari, ni banga abun boye-boye a nan ba". Da fadar haka suka kwashe da dariya Kubura ta ce, "Kin manta ba jari kadai ba harda biyan bashin yar tinkiya da ta cinye". Salla-lami Ladi ta kwasa tana tafa hannu "Ashe dai abinda mutane suka fada gaskiya ne, haba Fatsuma wallahi kin ci amana kuma kin bani kunya, ni sam banyi zaton haka daga gareki ba. A ina ma aka taba haka taya zaki kama dukiyata ki ba mijinki ya sayar ba tare da sanina ba?". Kuka Fatsuma ta fashe da shi irin mai sosa zuciya, ta kalli Ladi cikin hawaye ta fara magana, "Don Allah kiyi hakuri Ladi na rantse miki da Allah duk abinda ya faru ba da sa hannuna ba kuma ba da yawuna ba, son zuciyarsu kawai suka aikata amma wallahi ba ni nace su kama miki akuya su sayar ba, babu irin magiya da roko da banyiwa Baban Zubairu ba amma baiji ba haka ya kama akuya yaje ya sayar tun jiya na rasa da wane ido zan kalleki har in miki bayanin wannan lamari shiyasa na kasa zuwa gidanki".


Ladi ta ce, "Fatsuma kin gama dani kawai amma wallahi ko sama da kasa zata hade sai an biyani akuyar nan don ba yafewa zanyi ba, ni kaina su kadai ne dukiyar da na mallaka nake tanadi nayi auren diyata da su idan Allah ya musu albarka, to a na me za'a kama min akuya a sayar wallahi a fito min da kudina. Kuma itama dayar akuyar yanzu zan kamata in tafi da abuna don ba zan bari ba watakil satin sama itama a kamata a sayar". Shiru Fatsuma tayi tana kuka yayin da Ladi ta mika mata hannu hade da cewa "Fatsuma bani kudina ko kuma ki bani akuyata". Shiru tayi domin ta rasa me ma zata ce, nan ita kuma Ladi ta hau jaraba ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba. ana cikin hakan ne suka ji shigowar Bukar yana tafe a hankali tamkar kazar da kwai ya mace wa a ciki, ya nufi madaka ya zauna a gefen turmi yana kallon mutane daya bayan daya. Daga ganin shi Fatsuma ta je da sauri ta durkusa a gabanshi tana kuka.


"Baban Zubairu kayiwa Allah da Annabi ka kawo kudin akuyar nan a bawa Ladi kayanta ga ta nan tun dazun take jira". Wata irin tsawa ya daka mata wanda ba ita ba su Kubura dake gefe ma sai da suka zabura, sannan ya dora da magana cikin masifa, "Wane kudi zan bada? Ai nine kudin gani nan sai ki dauke ni ki bawa Ladin". Ya ja tsaki kana ya dora da cewa "Wallahi yanzu na fara yarda da maganar su Kubura a kanki, da alamu ke mayyar ce da gaske ma ba sharri suke miki ba. Ina sauka fa daga mota dubawar da zanyi haka sai gani nayi aljihuna a yanke wai an sace kudi, shiyasa ban zargi kowa ba sai ke Fatsuma, watakil tunda na tafi kike mun mummunar addu'a shiyasa ma barayi sukayi nasarar sace kudin". 


Gaban Fatsuma ne ya sake faduwa, nan take ta shiga kokarin tattaro natsuwarta sannan tayi kokarin hada kalmomin da yake fada domin ta fahimci inda maganar ta shi ta sa gaba, wato yana so ya ce an sace kudin. "Innalillahi wa inna illahir raji'un" Suka dauka kusan tare ciki kuwa harda Ladi da ta kasa ta tsare tana jira a bata kudin akuyarta. "To na rantse da Allah baku isa ba idan ma wani shirin kuka hada domin a cinye min kudi tun safe ku canza shiri domin ba yafewa zanyi ba, wallahi a fito min da kudina ko kuma daga nan ma ina fita wajen mai gari zan tafi in kai kararku". "Salama Alaikum! - Salama Alaikum!". Daga waje suka ji ana sallama, daga zaune Bukar ya amsa yana mai tambaya waye, daga can yaji ance, "Malam Bashir ne, ka fito yanzu mu tafi fada Mai Gari yana nemanka yarka Mairo ta kai kararka wajen Mai Gari". 


Shiru sukayi suna bin juna da ido na yan dakiku domin jin zancen sukayi kamar wata almara, musamman Fatsuma da ta cigaba da nanata maganar a zuciya, "Yarka Mairo ta kai kararka!". Tunani take a zuciya anya kuwa Mairo dai babynta? Yanzu Mairo har tayi wayon da zata kai karar wani wajen mai gari kuma a tsaya a saurareta, to wai ma a kan me Mairo zata kai karar mahaifinta wajen Mai Gari?


"Fito Malam Bukar kai nake jira ku taho tare da Fatsuma zan biya gidan Ladi itama Mai Gari yana son ganinta". Jinjina kai Bukar ya shiga yi shima yana maimaita abun a zuciyarsa, don haka ya san inda maganar ta dosa tunda yaji Malam Bashir ya ce zai biya gidan Ladi, Fatsuma ta sako hijab tare suka fita Ladi tana cewa ai gata itama ba sai an biya ta gidanta ba. Kubura da Laure ma daukar gyaluluwansu sukayi suka ya fa suka bi bayansu Fatsuma suna ta fadin bakakken maganganu a kan Mairo.............


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Comments