ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 27

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-27-hausa.html


*^ Part 27 ^*



Boka Kare Dangi ya daga hannu ya kwadawa Aljani Duduge mari, hade da cewa, "Ku wawayen ina ne kuyi gaggawar binta ku kamo ta a yau nake so ta bar duniya". Aljani Duduge ya ce, "Kayi hakuri Boka wannan yarinyar ta riga ta gudu, duk da kasancewarmu Aljanu kuma ifiritai ko da mun bita ba zamu iya kamota ba don yanzu haka ta bace ta bayyana a wani waje na daban, bayan haka kuma a yanzu ko da mun kamota bana tunanin zamu iya kasheta domin yarinyar taurin rai irin nata gabaki dayan mu ya bamu tsoro, kashe wannan yarinyar sai anyi babban shiri". Da jin haka Boka Kare Dangi ya daga kai sama ya dinga kwarara ihu na takaici. 


Aljana Safuratu bata koma wajen Murja ba sai da ta samo magani ta saka a ciwukan jikinta, kuma har lokacin da ta koma Murja bata tashi daga bacci ba, don haka itama ta kwanta a kusa da Murja gefen dutse saboda yadda jikinta yake mata ciwo. Washe gari da safe Murja ta farka, ji tayi kanta na matukar ciwo duk jikinta ma ciwo yake yi a hankali ta tashi tana duban jikinta cikin mamaki da kidima da kuma tsoro. Kokonto take shin wannan jikinta ne kuwa? Me ya faru da ita? Ji take tamkar tayi wani nanauyan bacci yanzu ne ta farka sai kuma ta tsinci kanta a wani yanayi mai ban mamaki domin a sanin kanta ita yarinya ce da bata wuce shekaru 13 ba gashi yanzu ta tsinci kanta a cikin gangar jikin mace yar kimanin shekara talatin harda dori. Kuka kawai ta fashe da shi tana kokarin tuna abinda ya faru ko kuma matakin da take a halin yanzu a rayuwa, amma ina tunaninta na baya ne kawai yake dawo mata kwakwalwa ga kanta sai faman ciwo yake. 


Hankalinta bai kara tashi ba sai da ta kai duba zuwa ga kayan jikinta, saboda tsabar datti ba'a iya gane kalar kayan, zani a yage rigar ma duk a yayyage, farcen hannunta ta gansu zankala-zankala gashin kanta kuwa da ta taba a cukuikuye tamkar an nade tsohon tsumma. Kuka kawai ta kara fashewa da shi a karo na biyu yayin da take kara karewa wajen da take kallo, saman dutse ne babu alamar mutane a wajen, yanzu ta fara zargin kanta tabbas hauka take amma da alamu yanzu hankalinta ya dawo jikinta. Kifa kanta tayi a kan gwiwoyinta tana kuka, kamar daga sama taji an tabata ance, "Murja!". Da sauri ta ja da baya tana kallon wacce ta tabata a tsorace. Budurwa ce kyakkyawa yar kimanin shekara 22 wacce ke sanyi da abaya baka. Murja ta fara fadin, "Wacece ke? Me yake faruwa dani? Ya akayi kika san sunana? Kuma wa ya kawo ni nan?". 


Budurwar ta ce, "Ki kwantar da hankalinki yanzu zanyi miki bayanin komai dan Allah karkiji tsoro. Sunana Safuratu da alamu kinyi shekaru da dama a cikin lalura irinta hauka amma yanzu Allah ya baki lafiya kuma ni ce na tsinceki haka zalika insha Allah ni ce zan mayar dake gida". Da gama fadar haka Safuratu ta ga Murja ta kara gigicewa alamun tsoro sun kara bayyana a fuskarta, nan take ta fara fadin, "Ba zanje gida ba don Allah baiwar Allah karki kaini gida, kasheni zatayi wallahi gwara in cigaba da haukan da in koma gida". Safuratu ba karamin mamaki tayi ba, jin irin furucin da yake fitowa daga bakin Murja, tasan cewa lalai akwai wata a kasa tunda ta ji Murja na tsoron komawa gida. Safuratu ta mikawa Murja wata yar doguwar leda dake rike a hannunta, ta ce, "To kwantar da hankalinki karbi ledar nan a ciki akwai kaya da kuma kayan wanka ki gangara bayan dotsen nan akwai ruwa a cikin wani rafi kiyi kokari kiyi wanka sannan ki canza kayan jikinki". 


Murja ta karbi kayan a tsorace tamkar ba zataje ba, don zuwa lokacin ita tsoron Safuratu ya fara kamata, ta ya za'ayi mace budurwa kamar wannan ta zo cikin kasurgurmin daji irin wannan ko da yake tana jin karar motoci jefi-jefi da alamu akwai titi a kusa amma duk da haka tana mamakin Safuratu. A haka ta karbi kayan a tsorace ta zagaya tayi iyakacin iyawarta wajen wankan, domin ɗaudar dake jikinta tayi yawa sai a hankali zata fita, bayan tayi wanka ta saka kaya ta sake haurawa kan dutsen ta sama Safuratu a zaune ta zuro kafafunta kasa daga kan dutse, Safuratu na ganinta tayi murmushi hade da zuwa ta taryota hade da cewa, "Kai datti babu kyau ji yadda kika koma santaleliyar budurwa bayan kinyi wanka". Dan murmushi Murja tayi, yayin da Safuratu ta jata suka zauna bayan dan lokaci cikin shiru Safuratu ta katse shirun da cewa, "Kiyi hakuri nasan kinda da tarin tambayoyi da yawa a gareni, kamar yadda nima nake da tarin tambayoyi a gareki. Amma kiyi hakuri ki adana naki tambayoyin tukkuna ki amsa mun tambayoyina domin ni da sannu zaki san ko ni wacece, tambaya ta farko na ji kince bakya son komawa gida ko miye dalili?".


Murja ta sadda kai kasa nan take hawaye suka gangaro daga idanunta, yayin da abubuwan da suka faru a rayuwarta a lokacin da take da hankali suke dawo mata sabbi a kwakwalwarta. Ta kalli Safuratu cikin hawaye hade cewa, "Labarina mai tsawo ne amma zanyi kokari na baki labarin duk abinda na rike a kwakwalwata da kuma dalilin da yasa bana kaunar komawa gidanmu na gwammaci in cigaba da rayuwa a cikin hauka har in mutu a kan in koma gidanmu". Safuratu ta ja dogon lumfashi hade da cewa, "To fa, kawo hannunki in fara yanke miki wannan dogon farcen sai ki cigaba da bani labarin". Ba gardama Murja ta mika mata hannun sannan ta fara da cewa. 


"Sunan Babana Alhaji Rabe, shine mutumin da ya fi kowa kudi a garinmu na Kuje, mahaifiyata ta rasu tun ina karama amma babana ya ki yarda ya kara wani auren saboda tsabar son da yake min, a cewarsa zai iya auro wata ta shigo gidan ta cutar dani. Shiyasa a maimakon hakan sai dai ya dauki yara yan mata masu aiki da kuma kula dani idan baya nan, suma da zarar lokacin aurensu yayi, ko kuma ya ga ta zama budurwa babba sai a canza wata. A cikin haka aka daukko wata yar aiki daga wani kauye, Sunanta Lami itama mahaifiyarta ce ta nemi alfarma a dauketa aiki a gidan. lokacin yarinya ce Lami itama bata isa aure ba cikin lokaci kankani muka shaku da ita fiye da yadda nake shakuwa da sauran yan aiki ya kasance bacci kawai yake rabamu da Lami shima saboda a wajen Abbana nake kwana".


Lokacin da Lami ta isa aure sai Babana ya yanke shawarar aurenta kawai domin ganin irin shakuwar dake tsakaninmu yana ganin zata iya rikeni amana. Kasancewar duka iyayen Babana sun rasu kuma bashi da yan uwa da yawa sai yayanshi daya Alhaji Sadi, da ya kaiwa Alhaji Sadi maganar auren Lami a nan sukayi fata-fata domin shi Alhaji Sadi so yake Babana ya auri yar abokinshi shi kuma babana ya nuna musu ya fi yarda da Lami saboda zata fi rikeni da kyau. Daga karshe dai haka suka rabu Alhaji Sadi yayi ikirarin babu shi babu babana idan har ya auri Lami. Hakan baiyiwa babana dadi ba amma ba yadda ya iya haka ya hakura da dangantar. Cikin lokaci kankani aka daura auren babana da Lami daga bangaren gidansu Lami babu abinda sukayi hatta abinci babana ne ya dauki nauyi domin dama Lami marainiya ce babanta ya mutu kuma ita kadai ce a hannun mahaifiyarta.


Bayan aurensu da Babana ko shekara ba'ayi ba na fara fuskantar canjin hali daga Auntu Lami, domin abu kadan zanyi ta kyare ni, haka zalika sau da dama idan naje na zauna kusa da ita sai ta kyareni ta koreni ko ta ce na takura mata. Ana cikin hakan ne ta nemi alfarma a wajen Babana akan tana so ta dawo da mahaifiyarta gidan, amma Babana ya ce bai aminci ba amma ya mata alkawarin gyara musu gidansu dake kauye hakan bai mata dadi ba don haka cikin kwana biyun sai da ta kara matsawa a kan tsangwama da take mun. Cikin shekaru kadan mugun halin Lami ya bayyana ya kasance hatta Babana ya fahimci irin mugun halinta da kuma yadda take takura min a cikin gidan.


 Domin idan baya gida tamkar yar aiki haka take mayar dani a gidan, ina matukar wahala, na sha fadawa Babana yana cewa zai dauki mata don haka ya fara shawarar kara aure shi da abokinshi ba tare da sanin Lami ba, amma cikin lokaci kankani sai maganar auren ta mutu, ya ji baya son kara auren, hakan ta sha faruwa wanda shi kanshi yana mamakin abinda ke hanashi kara auran. Lokacin da na cika shekara goma ne Babana ya fara tunanin sakin Lami saboda kullum cin zalin Lami karuwa yake a gareni, domin duk sauran bakaken halinta basa damunsa abinda ke damunsa kawai irin mugunta da zauncin da take mun. Yasan cewa marowaciya ce lamba daya, kuma ya san cewa tana daukar abinci ta kai gidansu, sannan zuwa lokacin bata bin umarninsa ko kadan duk sanda ta ga damar fita to fitarta take, a cikin gari ma har rade-radin tana bin bokaye ake.


Sau da dama a gabana Babana yake rubuta mata takardar saki amma sai yaje gabanta sai ya kasa bata, ko kuma in yayi niyar furta mata kalmar saki sai ya ji bakinsa ya kasa fada. A haka dai muka cigaba da rayuwa duk da kasancewar kullum bakin halin Lami kara yawaita yake. Watarana na shiga dakinta domin kai mata lemun da ta aikeni in sayo mata, na shiga dakin na tarar tana waya ba tare da ta san na shiga dakin ba, naji tana cewa, "Wallahi so yake ya sakeni, ba dan aikin da ake yi a kanshi ba da tuni ya sakeni, don haka ki cewa Kare Dangi ayi gaggawar kasheshi idan ya mutu komai nashi ya zama nawa kuma zan bada tukwici mai kauri". Tana gama fadin haka ta bushe da dariya a lokacin ne kuma ta juyo ta ganni a tsaye..............


🙄 Na gaji

Comments