ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 34

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/xFXTeTEKb1U

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-34-hausa.html


Kai Murja ta daga sama tana karewa gawar Idi Mugu kallo, yadda jini ke zuba daga gabanshi inda Safuratu ta yanke. Ga dai gawarshi nan rataye a sama kamar ba shine baya da mintuna ashirin yake jinsa a matsayin dan ta'adda mai cikakken matsayi wanda daukar rayuwar wani a wajensa bai dauke shi a bakin komai ba, kuma kamar ba shine mutumin da yayi kokarin lalata mata rayuwa yanzu ba. Wani gwauron lumfashi ta sauke, nan take ta kai dubanta a dan tsorace ga Safuratu da ke kallonta tana murmushi, tabbas yanzu ta gama yarda cewa Safuratu aljana ce, a cikin aljannun ma tana da karfi ko kuma wata baiwa daban, in ba haka ba taya zata kashe mutum haka cikin dan kankanin lokaci. Safuratu ganin Murja tayi nisa a duniyar tunani ya sata katse mata tunanin da cewa, "Ke kuwa Murja me kike tunani haka kinyi shiru hade da zuba min idanu ko kiftawa bakya yi?". Murja ta danyi yake hade da sosa kai ta ce, "Tunani nake idan ke aljanace da gaske me yasa mutane suke iya ganinki, bayan kuma idanun mutum basa iya ganin aljani?"  


Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Eh ai wannan suffar ta yan adam ce ba asalin suffata. Don da a salin suffata nake ba zaki iya ganina ba, ba don kin dade a cikin hauka ba da ina iya cewa zuwa yanzu kin sha jin labarai na zamanin da can baya da aljannu suke yin suffar bil adama su shiga cikin mutane ba tare da an gane su aljannun bane". Murja ta ce, "To amma ke me yasa kike bayyanawa mutane cewa ke aljana ce, bakya tunanin za'a ji tsoronki kuma a kyamace ki? Don ko ni nan wallahi maganar nan da muke a tsorace nake jinina a farce yake watakil da zanji kwakwaran motsi zan iya zurawa a guje ko kuma nayi suman tsayi" Safuratu bata san lokacin da ta gaggabe da dariya ba, ta dade tana yi harda rike ciki, dariyar har sai da ta tsorata Murja ta fara ja da baya tana kallon Safuratu a tsorace, Safuratu cikin dariya ta ce, "Tsaya-tsaya dan Allah karki zuba a guje ko ki suma a cikin dajin nan kinga ni ba likita bace balle in baki tallafin gaggawa, amma wallahi kin bani dariya sosai". 


Murja ta ce, "Ai gaskiya na fada, aljana fa? Ai abun al'ajabi ne a gareni ace gashi muna magana da aljana tana kallona ina kallonta". Sassaita dariyar Safuratu tayi hade da cewa, "Allah sarki Murja ke da kika kwashe tsawon shekara 18 tare da aljana ai bai kamata kiji tsoron aljani ba". Murja tayi shiru tana tunani, can kuma sai ta dago hade da cewa, "Kina so ki ce, rayuwar da nayi ta hauka gaba daya ina tare da aljana?" Safuratu ta ce, "Kwarai kuwa ita ce ma ta haukatar dake, haka zalika ba kowa ya dauki nauyi haukatar dake a wajen boka ba face Auntynki Lami". Hawaye suka fara zarya a fuskar Murja hade da cewa, "A zahiri nayi tunanin ciwon haukana cuta ce kawai daga Allah, ashe ba haka bane Aunty Lami ce sanadi. Tabbas aunty Lami ta cutar da rayuwata, cutarwa mafi kololuwa kuwa, domin zuwa yanzu na girma amma bani da isashhen ilimin addini da na zamani, haka zalika ni ba bautar gidan miji ba. Wato dai ta so burin ta ya cika na salwantar da rayuwata, da haka ai da kasheni tayi kawai da ya fiye mun sauki".


Safuratu ta ce, "Allah ne bai bata iko ba amma abinda ta so kenan". Ta danyi shiru tana tunani sannan ta ce, "To ina Aljanar da ta haukarta da ni?". "Ai na dade da kasheta labari ne mai tsawo munsha artabu da ita da bokanta, a takaice ma ba dan makircin da suka kulla min ita da bokanta suka daureni na tsawon shekara 18 ba, da tuni na dade da cetonki daga ciwon hauka". Murja ta ce, "Allah sarki gaskiya da za'a sama aljannu irinku da abubuwa da yawa sunyi wa mutane sauki, ban taba sanin akwai aljannu irinku a duniya ba". Safuratu tayi yar dariya hade da cewa, "Ai kuwa akwai irinmu da yawa sai dai mafi yawanci sunfi taimakon wanda suke tare da su ta wata siga daban, kamar misali suna taimakon yan adam dangane da abinda ya danganci sihiri ko kuma wata cutarwa ta aljani. Amma ni na zabi na taimaki wanda Allah ya nufa da in taimaka ne kawai ta ko wane siga, yanzu haka sunan da na fi so bayan Safuratu shine ALJANAR FATIMA". Murja tayi saurin cewa, "Wacece kuma Fatima? Itama aljanar ce?". 


"Ba aljana bace mutum ce kamarki, yanzu haka tsawon shekara 18 rabona da ita, so nake in ga komai ya dai-daita a bangarenki sannan in koma gidansu na tabbatar tana cikin koshin lafiya domin bana tunanin su Mama Asiya zasu sake yunkurin cutar da ita a rayuwarsu bayan irin horon da nayi musu". Murja tace, "Wacece kuma Mama Asiya". Murmushi Safuratu tayi hade da cewa, "Kishiyoyin mahaifiyar Fatima ce, ita kuma Fatima marainiya ce, shiyasa suke zalintarta sosai ni kuma na bi ta hanyar diyar robarta na shiga gidan nake taimaka mata, labarine mai tsawo". "Wallahi har naji ina so in ga Fatimar nan don har ta shiga raina". Safuratu ta ce, "Karki damu insha Allah wataran zamu kawo miki ziyara tare da ita, watakil tayi aure ma zuwa yanzu". Murja ta ce, "Allah sarki". Safuratu ta ja lumfashi hade da cewa, "Kinga tunda na fahimci yanzu kin daina jin tsoron nawa, yanzu so nake ki koma sansanin masu garkuwa da mutanen can ki je ki ce musu wani ya kashe Idi Mugu, nasan zasu iya yo gayya domin su zo daukar fansa daga nan ni kuma sai in hallaka su baki daya, bana so in musu shigar bai daya ne a sama matsala da ta ka iya jawo asarar ran mutanen da sukayi garkuwa da su, shiyasa nake bin hanyoyin da zasu karar da su da kadan-kadan".


Cikin gamsuwa Murja ta kada kai, hade da cewa, "To amma kina ganin idan naje ba zasu rike ni su ce ni na kasheshi ba?" Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Karki ji komai ai ina nan ba zan bari wani abu ya sameki ba". Murja ta kada kai hade da nufar hanyar da zata mayar da ita sansanin yan daban. Zaune suke suna busa sigari wasunsu kuma wiwi suke busawa yayin da suka kewaye masu buga katin caca suna ta ihu hade da surutai irin nasu na marar kamun kai. Da gudu ta karaso wajen, tun kafin ta iso fiye da matasa biyar suka dana bindiga hade da saita ta da nufin bude mata wuta, ganin haka Murja tayi gaggawar daga hannaye sama hade da cewa, "Ni ce- Ni ce!" Wani mummunar dan ta'adda da ya dana bindiga kadan yake jira ya harba ya ce, "Kece wa kuma me ya kawo ki sansanin nan?". "Aa ke ba kece yarinyar da Idi Mugu ya ja yanzu kuka shiga daji ba ina yake Idin?". Murja cikin nishin karya hade da nuna alamun tsoro ta fara nuna hanyar dajin hadin da cewa, "Wani ya kasheshi, yana can a rataye a kan bishiya kuma wanda ya kasheshi ya ce in zo in fada muku kuje ku daukko gawarsa". Wani irin mugun ashar daya daga cikinsu ya danno hade da kwarara ihu, "Na rantse da mai sama yau sai bindigata ta zubar da jini, nasan ba aikin kowa bane aikin yaran sansanin dabar Dodo ne". Da fadar haka kusan yan ta'addan sha biyar suka saba bindigoginsu a kafada hade da saka Murja gaba domin ta kaisu inda aka kashe Idi Mugu. 


Tafe suke Murja a tsorace tana dube-dube har suka karaso wajen, daga kai sukayi suna karewa gawar Idi Mugu kallo, tabbas basu ga alamun harbin bindiga a jikinsa ba, amma sun ga azzakarinsa a yanke. Wani dan ta'adda mai jajayen idanu ya juya ya shaki wuyar Murja, hade da zare mata jajayen idanunsa masu kamar garwashi ya ce, "Ke don ubanki fada mana gaskiya waye ya kashe Idi? Domin babu alamun harbin bindiga a jikinsa kuma na tabbata irinku ko ku goma ne ba zaku iya yiwa Idi irin wannan kisa na wulakanci kuma har ku iya daure shi a sama ba". Murja ji tayi ta kasa yin lumfashi saboda irin shakar da yayi mata, nan take ta fara tari wasu kuma suka hau bishiyar domin saukko da gawar Idi Mugu. Ji sukayi kawai ance, "Nine nan na kasheshi?". Ko da suka kalli saitin inda maganar ta fito sai su ka ga ba kowa bane face Gwaska, tsaye yake ya na rike da bindigarsa. 


Nan take zuciyoyinsu suka kama tafarfasa, mutum uku ne daga ciki suka haka bindiga hade da saita kan Gwaska suka bude masa wuta, amma da hayaki ya lafa sai su ka ga Gwaska yana nan tsaye a inda yake, don haka cikin fusata wasu ma suka sake saita Gwaska hade da bude masa wuta amma su ma tamkar na farko, sai tarin harsasan bindiga a gabanshi amma jikinshi ko kwarzane babu. Nan take wani marar kunya daga cikinsu ya fito hade sa cewa, "Au ashe yan sansanin dabar Dodo sun fara shan maganin bindiga, amma yanzu zan karya ko wane kalar asiri ne". Yana fadar haka ya ajiye bindigarsa hade da yi mata fitsari a gabansu ko kunya bai ji ba, yana gama yi wa bindigar fitsari ya dauketa hade da cewa, "Gwaska akwai wani abu da kake so ka fada, wanda zai zama kalmarka ta karshe a duniya? Idan akwai kayi gaggawar furtawa domin yanzu zan aikaka kiyama kuma shine kadai adalcin da zan iya yi maka". Murmushi kawai Gwaska yayi hade da cewa, "To bismillah". Ko rufe baki bai gama yi ba, yaji saukar harsashen bindiga, ji kake rataatatata! Sai da bullet din cikin bindigar ya kare baki daya sannan mutumin ya dakata. Ido ya zaro bayan ganin Gwaska a tsaye ko kwarzane babu a jikinsa.


 Gwaska ya ce, "Tunda ka gama naka yanzu zagayena ne". Da fadar haka ya daga bindigarsa hade da saita kan wannan dan ta'adda ji kake shuut! Tuni bullet ya ratse ta cikin kansa nan take ya fadi kasa matacce, ko da ganin haka sai ran yan ta'addan ya kara baci, suka dura harsasai a cikin bindigunsu hade da budewa Gwaska wuta ba ji ba gani, sun dade suna yi daga bisani suka nami Gwaska sama ko kasa suka rasa. Wata dariya marar dadin saurare ce ta ratsa kunnuwansu, yayin da suka ga wani hayaki da basu san ko daga ina ya fito ba, hayakin ya cika wajen ya kasance ko mutmin dake kusa da kai baka iya gani....................


😂 Yauwa na san kuma kun gaji, to mu hadu gobe in mun huta nima na gaji

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments