ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 35


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/bUybxojRV7g

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-35-hausa.html


*^ Part 35 ^*


Murja da ta samu bayan dutse ta labe tana kallonsu, bayan hayakin ya lulube wajen sai ji tayi sun saki harbin bindiga ta ko'ina, a cikin hakan wasu daga cikinsu suka harbe junansu basu sani ba, yayin da sauran kuma mutum yana tsaye yana harba bindiga sai dai yaji hannu ya zuro daga sama ya murde masa wuya. Cikin dan kankanin lokaci wajen yayi tsit tamkar ba kowa, hayakin yana daukewa Murja ta hango gawarwakin wadannan yan ta'adda gabaki daya a kwance a kasa, wasu sun harbe junansu wasu kuma Safuratu ta kashe su, ji tayi ance "Kai!" Da karfi daga bayanta nan take Murja ta zunduma ihu hade da cewa, "Wayyo Allah na". Tana juyawa ta ga Safuratu ce, ai kuwa Safuratu ta fara kyalkyala dariya hade da cewa, "Tsoro ya miki yawa Murja". 


Murja ta ce, "Irin wannan ai sai ki sa mutum ya suma, wallahi nan a matukar tsorace nake musamman yanda naga hayaki ya bayyana ya zagaye wajen ga karar harbin bindiga da ban saba ba, kunnuwana har wani irin dauuu! Suke". Murja ta ce, "To yanzu in sake komawa sansanin yan ta'addan ne in taho da wasu?". Safuratu ta ce, "Aa rabu da su zasu kawo kansu da kansu idan suka ga wadannan din basu koma ba". Waje suka samu suka zauna suna ta hira bayan Safuratu ta je ta kawo musu abincin, suna wajen har dare yayi ba su ga ko daya daga cikin yan daban ya zo ba, Murja ta ce, "Da alama yan daban nan basu damu da yan uwansu ba, kinga har yanzu dai ko kiyashi bai zo ba, gwara mu tashi mu tafi kar dare ya mana a daji". Safuratu ta ce, "Tukunna dai ba yanzu zamu tafi ba, mu dan kara jira ina ji a rana zasu iya tahowa nemansu". Murja ta ce "to". Wajejen karfe 8 da rabi na dare suka ji karan mashin na nufowa inda suke, dama dai suna jin karan daga nesa amma wannan karon ta bangarensu ya nufo don haka Safuratu ta kama Murja sai gasu a saman bishiya.


Gudu yake da mashin yana dube-dube, bai ankara ba ya ci karo da wani abu, wanda ya sa mashin din yayi sama hade da watsar da su a kasa, nan take suka mike hade da kakabe jikinsu suna duba abinda ya kada su din, bayan haska fitila nan take idanuwansu suka fara gane musu gawarwakin mutane, da suka haska fuskar daya nan take suka ga ashe dan Ta'addan sansaninsu ne, da faruwar haka suka hau dube-dube basu ga kowa ba, nan take suka yanke shawarar kirayo sauran, don haka suka daga bindigunsu sama suka rika harbi daya bayan daya. Su Safuratu suna sama suna kallo ba jimawa sai ga mashina na fitowa ta ko'ina wanda sun kai su mashin ashirin ko wanne dauke da mutum daya rike da bindigu a hannu. Suna karasowa suka sassauko daga mashinan bayan ganin gawarwakin yan uwansu, nan take suka daga bindigu sama suka rika harbin iska hade da ihu irin na takaicin rashin yan uwan nasu, Safuratu na ganin haka ta ce wa Murja "Duk abinda zai faru ki tsaya a nan karki je ko'ina". Murja ta amsa da "To". Hade da kara rike katon rashen bishiya da take kwance a kai.  


Daya daga cikin yan ta'addan dake faman dora gawarwakin yan uwansu a kan mashin domin tafiya da su gida ne yaji wani abu ya cije shi a kafa, nan take ya kwalla ihu, hade da zubewa kasa. Su duka suka juyo da hankulansu gareshi suna haskawa suka ga alamun ba lumfashi a tare da shi. Na kusa da shi ya taba shi hade da cewa, "Ya mutu wallahi". Basu yi wani yunkuri ba suka sake jin kusan mutum uku sun saki kara hade da zubewa kasa matattu, sai a lokacin suka ga wasu irin bakakken macizai na fitowa ta ko wane bangare suna kai musu farmakin sara. Ai kuwa suka haka binidigu suka rika harbin macizan amma sai macizan suka rika bacewa suna bayyana a gabansu hade da sararsu. Cikin lokaci kankani wajen yayi shiru baka jin motsin komai, Murja dake sama saboda tsabar tsoro a wannan lokacin ko jikinta ka yanka ba lalai ka sama jini ba, a bayanta taji ance "Ta shi mu tafi duk na hallakasu". Ai kuwa ta fasa ihu hade da sakin rashen bishiyar da ta rike ta yo kasa, da sauri Safuratu ta riko ta hade da direta a kasa tana mata dariya wai ta cika tsoro.


Gudu suke yara da manya, masu kudi da talakawa, irin gudun da ake kira na ceton rai, da yawa daga cikinsu sun gaji amma haka suka daure suna masu bawa kafafunsu hakuri domin sun san cewa ba lalai irin wannan damar ta sake samuwa a garesu ba, Safuratu ta kalle su cikin tausayi da yawansu iyayensu sun kasa hada kudin fansar da zasu cecesu, wasu kuma dangin nasu a halin da ake ciki suna can suna ta sayar da kadarorinsu domin samu su ceto su. Daga karshe dai gashi Allah ya bata ikon cetonsu, amma saboda yawansu ba zata iya daukarsu baki daya ta fitar da su daga dajin ba, don haka ta ce su biyota domin su fita daga dajin. Murja dake faman gudu ita kanta ta gaji daurewa take, ta kalli Safuratu dake gefenta hade da cewa, "Wai su yan ta'addan kina ganin zasu tashi kafin mu fita daga cikin dajin nan ne? Ni fa wallahi na gaji da gudun nan idan ba zasu tashi ba kamata yayi mu tsaya mu dan yi hutu ko na awa guda ne kafin mu cigaba da tafiya, kinga akwai yara da tsofaffi dan ma maza sun dauki wasu daga cikin yaran". 


Safuratu ta ce, "Gubar da na shaka musu ta bacci yan awanni ne kawai take yi, kuma kinga yanzu asuba ta kawo kai, ina fargabar su tashi su ga duk mutanen da sukayi garkuwa da su sun tsere su biyo sahu, kuma kinsan a mashina zasu biyo baya kinga kuwa babu wuya zasu iya isko mu, ni hallakasu a wajena ba damuwa bane, saboda sun kashe mutane sun cancanci mutuwa gaba dayansu, ni matsalata daya bana so su taba lafiyar daya daga cikin bayin Allahn nan shiyasa nayi kokarin kubutar da su ta wannan hanyar". Murja ta ce, "To wai yanzu idan munje bakin titi ya za'a da mutanen nan da yawa, a irin yawan nan namu mota ashirin ma ba lalai su kwashe mu ba". Safuratu ta ce, "Ai shiyasa nayi wa rundunonin tsaro magana, duk da na ga basu dauki maganar mai muhimmanci ba amma na basu adireshen wajen, idan sun zo abu biyu ne zai faru, na farko in damka musu wadannan mutanen a hannunsu, sannan in damka iyalan yan ta'adda kama daga yara da dokiyoyin a hannun hukuma". Gudun da suka kara bai wuce na rabin awa ba suka karaso bakin titi, inda nan take mutane suka rika zubewa kasa kwance rairas saboda gajiya.

Sun tsayar da motoci da yawa sun ki tsayawa saboda ganin irin yawan da suke da shi, zuwa can sai ga motocin yan sanda har mota biyar. Nan take Safuratu ta shaida musu cewa yan ta'addan na nan tafe, don haka jami'in ya fara waya hade da neman taimakon jami'an sojoji dake kusa da wajen. Jin maganar ba ta wasa bace ya sa aka tado kusan barrack din sojoji, yayin da motocin yan sanda suka hau jigilar kwashe jama'a. Tun daga nesa suka fara jiyo harbin bindigogin yan ta'addan wanda nan take suma sojojin suka fara harbi sama saboda ban tsoro. Ana fara hangen juna tsakanin sojoji da yan daban sai aka fara barin wuta ji kake harbin bindiga ta ko 'ina. Sauran mutanen da ba'a karasa kwashewa ba nan take sojoji suka umarce su da su kwanta a can bayan titi kar wanda ya yarda ya mike tsaye, a cikin hakan ne wani soja ya ga Safuratu a tsaye ta nufi bakin titi inda ake barin wuta, nan take ya daka mata tsawa hade da cewa, "Ke dan ubanki kina so ki mutu ne? Maza ki koma wajen yan uwanki ki kwanta". 


Safuratu tayi dariya hade da cigaba da tafiya, hakan ba karamin fusata shi yayi ba, don haka ya ta so da sauri hade da daga hannu zai sharara mata mari, charaf! Ta chafke hannun yayi-yayi ya kwace hannun ya gaza sannan Safuratu ta ce, "Kai dai ka cigaba da aikinka nima zan cigaba da nawa idan na mutu ba zan zargi ko daya daga cikinku ba". Da gama fadin hakan Safuratu ta saki hannunsa hade da falfalawa da gudu ta nufi wajen yan ta'adda, shugaban sojoji da na yan sanda dake labe-labe suna barin wuta ganin matashiyar budurwa ta zo ta wuce su a guje ya sa ya fara daka mata tsawa hade da zagi a kan ta dawo amma ina, ba zato ba tsammani sai gani sukayi tana gocewa harbin yan ta'adda yayin da ta tunkaresu gadan-gadan, wani irin tsalle suka ga tayi hade da gabzawa wani dan ta'adda dake faman harbinta ganin ta nufoshi naushi a fuska, nan take ya bi gi itaciya ya fado kasa jini na zuba daga baki da hancinsa. Tsit wajen yayi na yan dakiku, domin kuwa gaba daya sakin baki sukayi suna kallon Safuratu, da yan ta'addan da su Sojojin. 


Cikin zafin nama ta dauki bindigar dan ta'addan da ta kashe, hade da budewa sauran wuta, cikin lokaci kankani ta kusan karar da rabin yan ta'addan, domin duk wanda ta saita ta harba bullet daya yake aikashi lahira. Ganin irin barnar da take musu ya sa shugabannin yan ta'addan sukayi umarni da a koma baya. Nan take wasu suka juya da gudu a kafa wasu kuma suka hau mashina saboda sun tabbatar lalai wannan yarinyar ba mutum bace, in kuwa mutum ce to lalai aljani ne yayi mata horon yakin bindiga. Hankalinsu ne ya dada tashi ganin Safuratu ta dauki bindigu biyu hade da rufa musu baya, nan take suma sojajin da suka ja daga suka rufa mata baya ganin ta kora yan ta'addan. Gudu suke a matukar tsorace domin ceton rayukansu kai kace wani katon dodo ne ya biyo su, masu mashinan kansu gudun da suke ba na wasa bane, amma haka Safuratu ta rika binsu da masifaffen gudu tana hankadesu da su da mashin nan. Ganin babu matsera ya sa Zaki, Dodo, Da Goje suka tsaya hade da zubar da makamansu suna daga hannuwa sama suna fadin "Dan Allah karki kashe mu munyi saranda" 


Safuratu ce ta karaso wajensu hade da cewa, "Na tabbata mutane da yawa sun muku roko makamancin wannan amma baku fasa kashe su ba, don haka nima banga dalilin da zai sa na barku ba". Dodo cikin tsoro da kaduwa kamar ba shine shugaban yan ta'adda dake ji da tsageranci ba, ya ga mutuwa tsirara duk ya fita hayyacinsa ya ce, "Dan Allah karki kashe mu ki yafe mana, mun tuba ba zamu sake harkar ta'addanci ba idan har kika kyalemu baki kashe mu ba, mun yarda mun mika wuya ki mika mu ga jami'an tsaro suyi mana duk hukuncin da ya dace damu". Safuratu ta gaggabe da dariya ta dan jima tana yi tukun ta ce, "Ai ni ce zan yi muku hukunci irin wanda Allah ya ce ayi dai-dai da aikin da kukayi. Na tabbata idan na mika ku ga jami'an tsaro ba lalai a kashe ku ba, ana iya yi muku daurin rai da rai, ko kuma a deba muku shekaru a gidan yari daga karshe ma ana iya yafe muku, ni kuma banga amfanin wannan ba saboda zuciyoyinku baki daya bakake ne babu alkhairi ko kadan a ciki"
Ran Goje ne ya fara tafasa saboda tsabar baci, wai ace duk tsabar tsageranci da rashin mutunci irin wanda sukayi a baya, amma yau mace macen ma budurwa ita ce take neman ganin bayansu har ta kai sun tsuguna kasa suna rokonta a kan ta yi musu rai? Ji yayi kawai zuciyarsa ba zata iya dauka ba, don haka cikin zafin nama yayi kukan kura hade da lalubo bindigarsa nan take ya saita kan Safuratu ya harb.............


Sorry jiya dare yayi ban karasa typing ba, yanzu kuma na gaji 😂

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments