ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 49



🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/w0hnTVda2wQ 

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-49-hausa.html


*^ Part 49 ^*

Khalil ya fita ya nufi dakin Jamsy ya duba ko ina da yake tunani, amma baiga ko bera ba, don haka ya dawo ya ce wa Jamsy ta tashi ta koma dakinta kawai tsorata ne tayi, ita kuwa ta ce ta rantse da Allah ba zata fita ko ina ba a nan zata kwana. Ba yadda baiyi da ita ba amma ta ki yarda ta fitar mai daga daki dole ya hakura suka kwana a dakin. Washe gari da safe suna tsaka da breakfast duk wanda ya kalli fuskar Hajiya Lami ya san cewa tana cikin farin ciki, Mama Dije ta kasa daurewa hade da cewa, "Wai ni Lami fara'ar me kike tun da safen nan?". Cikin murmushi ta dubi uwartata hade da cewa, "Ke dai bari Mama wallahi ina cikin farin ciki abun nan ne ya samu". Bayan yin shiru na dan lokaci sai Mama Dije itama ta washe baki hade da cewa, "Au! ni har na sha'afa ma". Hajiya Lami ta ce, "Bari a daukko wayar aje a wanko su, ai ina tunanin yanzu za'a kira Inna Sailuba a fada mata tafiyar domin da zafi-zafi akan bigi karfe". Mama Dije ta ce gaskiya kam gwara a hanzarta ko ma huta da wannan jarabar a cikin gida". 


Khalil dake zaune yana kurbar shayi ya ce, "Mom ni ina jin sai wasu maganganu kuke amma na kasa fahimtar komai a ciki". Dariya Hajiya Lami tayi game da cewa, "Yaro man kaza, ai wannan zancen manya ne babu abinda zaka gane a ciki". Ta kai dubanta ga Jamsy hade da cewa, "Ke Jamsy maza tashi ki daukko min wayata a daki, ki hado da ta Mama Dije". Ba musu Jamsy ta tashi taje ta daukko wayoyin ta kawo mata. Tana yar waka cikin jin dadi ta bude wayar hade da shiga cikin hotuna, tsaye ta mike lokaci guda hade da cewa, "Kan uba!". Kallonta sukayi gaba daya, ganin duk wani murmushi da alamun farin ciki dake kan fuskarta ya bace, "Ke Jamsy uban waye yace ki goge hotunan Murja a cikin wayar nan ki dauki naki?". Jamsy ta kalli uwartata dake zare mata idanu hade da cewa, "Mom wane irin hotunan Murja kuma? Mai zai kai hotunanki cikin wayar Murja balle kuma har na goge su". Tsawa ta daka mata hade da cewa, "Yi mun shiru don ubanki wannan hoton waye? Idan ba ke kika goge hotunan ba uban me ya kawo hotunanki a cikin wayata?". 


Idanunta na kaiwa kan hotunan nan take ta fara karkarwa, ta fara nona hoton dake cikin waya da yatsa tana fadin, "Na shiga uku, Yaya Khalil ka gani ko? Dama na fada maka wallahi aljanar gaske ce ba tsorata bane nayi, domin jiya aljanar ce ta sa na dauki wadannan hotunan, wallahi aljanace". Kallo suka kama binta da shi baki bude, Mama Dije ta ce, "Ke dallah ki natsu kiyiwa mutane bayani wane irin aljana kuma?". Nan take Jamsy ta basu labarin abinda ya faru tsakaninta da aljana jiya da dare. Khalil ya kyalkyale da dariya harda rike ciki, ya fara nuna Jamsy da hannu yana cewa, "Banza matsoraciya Mom kuji wai Aljana, ko ina ta taba jin mutum ya ga aljana balle har suyi magana da ita mai tsawo haka". Shiru Hajiya Lami da Mama Dije sukayi domin su kam basu isa su karyata zancen aljana ba, domin an basu tsoro sunga aljanar da idanunsu ba sai an kara musu da labarinta ba. "Mama Kar dai ace aljanar da nake baki labari ta tsorata ni itace Jamsy take bayani?". Mama Dije tace, "Ba zan mu sa ba domin nima ganau ce ba jiyau ba, in da abin bai faru a kaina ba ina iya karyatawa, amma da gaske jiya naji ana buga kyauren dakina amma naki budewa nayi zaton ko aljanar ce".


Hajiya Lami ta dubi Jamsy hade da cewa, "Wai ita aljanar da kanta itace ta sakaki kika dauki wannan hotunan?". Cikin alamun kaduwa Jamsy ta ce, "Eh wallahi Mom kuma tace in rika zuwa wajen Umm tana koya min karatu idan banje ba sai ta ci ubana domin ta ce tana cikin gidan nan duk abinda nake tana kallona, wallahi bari ma na tashi tun yanzu na tafi". Jamsy ta fada hade da ajiye kofin shayi dake hannunta ta nufi kofar fita daga falon. Dariya Khalil ya kyalkyale da ita, domin jin abun yake kamar almara. Cikin dariya ya fara fadin, "Yanzu mama harda ku zaku biyewa shirmen Jamsy, wai aljana, ko waye ya fada mata ana ganin aljana". Mama Dije ta ce, "Rufe mana baki ja'iri kawai to ba shirme take fada ba, ni nan da idanuna na ga aljana tsakar dare ta buga min kyaure ina budewa na ga mutum ba kai". Dariya Khalil ya kara bushewa da ita, Mama Dije ta dauki cokali ta wurga masa hade da fadin, "Tashi ka bamu waje mahaukacin banza, Allah yasa ku gamu da aljanar daga nan ka rika dariya da daukar zance a matsayin shirme". Tashi Khalil yayi ya haura sama yana darisama


Hajiya Lami tace, "Mama maganar Jamsy abun dubawa ce fa, to amma me zai sa aljana ta goge hoton Murja da muka dauka kuma ta sa Jamsy ta dauki hotonta da kanta?". Mama Dije ta ce, "Tunanin da nake kenan ita aljanar ina ruwanta da hotunan Murja da muka dauka? Ko dai tare suke?". Hajiya Lami tace, "Wallahi na fi tunanin tare suke da aljanar, baki lura da abubuwan da Murja din take ba, wataran ki ga tana jin tsoronmu, wataran kuma ki ga idonta a bushe bata jin tsoro ko kunyar kowa". Mama Dije ta ce, "Eh bari in kira Sailuba kuwa ta zo dole mu san abin yi, domin in ya tabbata akwai aljana a tare da Murja ba dole mu dauki mataki a kanta". Tana gama fadar haka ta ciro waya ta lallatsa sannan ta kara a kunne. 


Da sallama ta shiga falon, baki daya suka dago kai suka kalleta harda Murja da ta bararraje a kan carpet tana cin doya da suka gama dafawa yanzu. Tsaye tayi kerere tana kare musu kallo a wulakance, "Ke Ummi zuwa nayi ki fara koya min karatu". Ummi da ba karamin tsoron Jamsy take ba, ta ce, "To Aunty Jamsy wane kalan karatu na islamiyya ko na boko?". Tsaki ta ja, "Mtseewww! Ke din banza zaki iya koya min karatun boko, ko kin manta yanzu haka jami'a nake? Karatun Islamiyya zaki koya min". Gaba daya mamaki ya cika su, tun daga kan Saratu, Murja da ita kanta Ummi din, basu san dalilin zuwan Jamsy ba amma sun tabbata ba a banza ba, duk da kasancewar yanzun ma da alama ba yan arziki ne suka kawota ba. Ummi ta ce, "To Aunty Jamsy yanzu dai nayi shirin makaranta, ko zaki bari in na dawo daga makaranta sai mu fara karatun?" Wani malalacin kallo ta bita da shi, lalai yarinyar nan bata san halinta ba ne, ba karamin juriya tayi na sauke girman kanta ba har ta yarda zata dauki karatu a wajenta, shine yanzu take fada mata wai makaranta zata wato tana nufin ta jira sai ta dawo kenan? "Ke Malama yanzu nake so mu fara, ba ruwana da zuwa makarantarki ko makararki". Ummi ta kalli mamanta kamar zatayi kuka, don zuwa lokacin ma ta makara, tayi niyar tafiya makaranta bata karya ba, amma Murja ta matsa mata a kan ta tsaya ta karya tukun. 


Murja ta kalleta hade da cewa, "Haba Jamsy kiyi hakuri mana ki bari sai ta dawo, nima nan zamuyi karatu amma saboda zuwa makarantarta yasa muka bari sai anjima". Cikin fusata Jamsy ta ce, "Dallah malama yi mana shiru ke kuma, wa ya kasa dake ma balle ki dauka? To ba za'a bari sai ta dawo din ba yanzu nake son a fara karatun. Ba don wani dalili ba ma ai yau din nan da sai sun bar gidan nan, ke ma ba kyaleki nayi ba dole zaki bar gidan nan idan mama ta kasa korarki ni zanyi maganinki". Juyawa tayi ga Ummi da nufin ta cigaba da balbaleta da masifa, abinda ta gani ne ya sata ja baya a tsorace tana karkarwa. Wannan matar ta gani tsaye a bayan Ummi tana harararta da kwala-kwalan idanunta. Hannu ta fara nunawa saitin matar tana fadin, "Aljana, ga ga aljana nan a bayanki".


 Gaba daya suka juya suka kalli inda ta nuna din basu ga komai ba, yayin da ita kuma ta ji matar ta daka mata tsawa hade da cewa, "Ashe dai horon da nayi miki jiya bai gamsar dake ba, kuma da nace ina kallonki duk abinda kike baki yarda ba?". Cikin tsoro da fargaba ta ce, "Wallahi na yarda na rantse da Allah na yarda". "Maza ki ba Ummi hakuri, sannan ki ce kin yarda ta je ta dawo daga makaranta". Bakinta har rawa take ta ba Ummi hakuri sannan ta ce ta je sai ta dawo daga makarantar. Gaba daya kallonta suke cike da mamaki abubuwan da take kamar zararriya, daga karshe ma gani sukayi Jamsy ta tashi ta ruga da gudu waje. Murja ta kalli Safuratu dake gefenta a tsaye wacce su Saratu basa ganinta, tasan cewa ba aikin kowa bane aikin Safuratu ne, Safuratun ma kai ta daga mata alamun itace....................


Nasan yayi kadan but nayi alkawarin yi yau ne. 


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments