*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/3JCxKvOVecs
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-51-hausa.html
*^ Part51 ^*
Kallonsa suke cike da mamaki yayin da shi kuma ya dage sai dukan iska yake da bindin saniya dake hannunsa, zuwa can ya ce, "Ku matsa mata hanya ga yar aljana nan zata wuce". Ai da gudu suka matsa daga saitin bakin kofar falo da suke har suna cin karo da juna. Zuwa yayi ya mayar da Bindin saniyar da ya daukko cikin jaka sannan ya ce, "Yanzu na kori kananun aljannun saura uwar ta su, domin ita wannan yarinyar da na kora yanzu ta ce min mahaifiyarta ce aljanar da take tsorata kuma, kuma ta ce min nan asalin filin da aka gina gidan nan a nan gidansu yake a jikin wata katuwar bishiya wacce aka sare, shiyasa ma yanzu suka ki barin waje". Hajiya Lami a dan tsorace ta ce, "To boka baka ganin mu sayar da gidan nan kawai mu tashi, tunda aljannun da yawa kuma sunce gidansu ne tun asali?". Buka ya kyalkyale da dariya, ya dan dade yana yi kuma sai ya tsuke fuska hade da cewa, "Karki damu Hajiya, yanzun nan zan kira aljanar a gabanku zan kuma koreta daga gidan nan". Sailuba ta ce, "Karki damu Lami ai tunda mai aljannu ya shigo gidan nan, na tabbata daga yau gidan nan ya haramta ga aljannu ko kofar gidan nan ba zasu kara zuwa ba.
Mama Dije ta ce, "Ai mu a fitar da su din dama muka fi so". Wani jan kyalle ya fiddo daga cikin katuwar jakar tashi dake cike da karikitai, ya shimfida a tsakiyar falon, sannan ya fiddo wasu layoyi guda uku ya jajjerasu a gefe da gefen kyallan. Suna tsaye suna kallon abinda yake ba su ce da shi kala ba. Ya fiddo wani abu a cikin kwalba mai gari ya barbada a kan kyallen sannan ya rufe ido ya fara karanta wasu irin sunaye wanda daga ji kasan na aljannu ne, ya dan jima yana yi ba zato ba tsammani sai gani sukayi kyallen ya mike tsaye tamkar mutum ne a cikinsa. A tsorace Jamsy ta labe a bayan Hajiya Lami tana leke, ba Lami ba gaba dayansu sunyi matukar tsorata, Dariya Naziru mai Aljannu ya kyalkyale da ita, sannan ya ce, "Yauwa gata ta zo". Mama Dije ta zare ido tana kallon kyallen, tabbas motsi yake yi tamkar mutum ne a cikinsa a tsaye. Naziru mai Aljannu ya kalli kyallen hade da cewa, "Ke malalaciyar aljana, kafin in fatattake ki in koreki daga gidan nan ina so ki fada min sunanki, kuma ki fada min shekarunki nawa".
Shiru yayi na dan lokaci hade da kasa kunne kamar mai sauraron wani abu, sai kuma ya juyo ga su Mama Dije ya ce, "Ta ce Sunanta Junaibatu kuma shekarunta dubu ashirin ba uku". Ya juya ga kyalle hade da sake cewa, "Miye dalilinki na zuwa ki tare a gidan mutane har ki rika tsorata su?". Kamar dazun shiru yayi ya kara kunne sannan ya sake juyawa ga su Hajiya Lami ya ce, "Ta ce nan asalin gidan kakannin kakanninta ne so take ku tashi ku bar mata gidanta, wai tayi alkawarin sai ta koreku daga gidan". Naziru ya juya hade da bata rai ya ce, "Karya kike malalaciyar aljana, yau din nan ina so ki tattara yaranki da duk wasu karikitanku ku bar gidan nan, idan ba haka ba kuma zan konaku gaba daya ke da iyalanki". Kamar almara sai ji yayi ance, "Ba zan fita daga gidan nan ba, kaine zaki fita yanzun nan, kuma ba zaka sake marmarin dawowa ba". Zare ido ya fara yi, yana kuma kara dubawa domin ya tabbatar abinda yake ji daga cikin kyallen nan yake fitowa. Amma shi sam baiyi tsamammin hakan ba, kwakwalwarshi ce ta shiga sake-sake domin bai gaskata ba, ya juya ya kalli su Hajiya Lami hade da cewa, "Ko kunji abinda naji aljanar nan ta fada?". Sailuba ta ce, "Mu ina mu ina jin maganar aljannu, ai kai kadai kake ji, mu sai ka fadi mana ne ma sannan muke sanin tayi magana".
Zagaya kyallen ya farayi a hankali yana kare masa kallo, tabbas abinda yake ciki yayi kama da mutum din gaske, "Miye a cikin kyallen nan?". Ya fada yayin da ya tsurawa kyallen idanu. Ba'a jima ba ya ji ance, "Ni ce nan, aljana Junaibatu". Tsoro ne ya fara shigarsa kar dai aje aljanar gaske ce a gidan, ya kai dubansa ga su Mama Dije da ke binshi da kallo a tsorace, domin tuni tsoro ya kama su. Shi kuma tunanin yadda zaiyi da lamarin abinda ke yi masa magana a cikin kyalle yake, don yana gudu ya nuna alamun tsoro ya ji kunya a gaban mutanen gida bayan kuma sunji sunanshi mai aljannu, ko kadan bai kamata ya ji tsoron aljannu ba. Zuwa can dabara ta fado masa, ya ce da su, "In san samu ne ku bani waje, ko dai ku shiga daki, ko kuma ku fita waje, domin aljanar nan ta na neman yi min taurin kai, ni kuma yanzu zanyi mata hayakin barkono dole ta bar gidan nan". Mama Dije ta ce, "Yauwa yaro ni dama nan duk a tsorace nake, bari mu fita mu baka waje zaka ma fi sakewa". Har rige-rigen fita suke daga falon suna waiwayen kyallen dake tsaye tamkar mutum ne a ciki yana motsawa.
Naziru mai aljannu da ya bi su Hajiya Lami da suke fita da kallo, juyowar da zaiyi sai gani yayi wutar falon ta dauke, kasancewar rana ce kuma tagogin falon a bude, yana iya ganin ko ina, bisa mamaki sai gani yayi labulayen dakin suna sauke kanshi, cikin lokaci kankani ya ga dakin yayi duhu, a hankali ya ga hannu ya zuro daga cikin kyallen ya yace kyallen. Idanunsa ne sukayi arba da wata mummunar mata, baka ce siririya idanunta kwala-kwala. Fuska sam ba kyan gani da wani dakusashhen hanci a tsakiyar fuskartata. Suna hada ido da Naziru mai aljannu ta wangale baki ta sakar mai wata irin dariya mai ban tsoro. Juyawa yayi da nufin ya ruga a guje ya fita daga cikin falon. Bisa mamaki ko tako biyu baiyi ba yaji an rike rigarsa. Wani irin ihu ya kwala, "Wayyo Allahna, don Allah ki sake ni wallahi na fasa korarki daga gidan". Naziru ya fadi haka yayin da ya juya baya yana kallon abinda ya rike shi, aljanar dai ya gani itace ta rike shi da hannu guda, amma ya kasa ko matsawa daga inda yake, duk da yunkurin da yake da dukkan karfinsa domin ya kwace ya ruga da gudu.
Murmushi ta sakar masa wanda ya kara wa fuskartata muni da ban tsoro, ta daga baki cikin wata irin murya tamkar ta dodanni ta ce, "Aa ba yanzu naji kana cewa zakayi min hayakin barkono ba? Bismillah kayi mana". "Wallahi na fasa aljana kiyi hakuri, kiyi mun rai, bansan kece a cikin gidan nan ba da ban zo ba wallahi". Aljanar ta ce, "Karka bani kunya mana, tsoron me kake ji, bayan naji ance sunanka Naziru mai aljannu , kuma ai kai ka kirayo ni a cikin kyallen nan". Cikin tsoro ya ce, "Wallahi aljannun karya ne, rufa ido ne kawai nake wa mutane don neman kudin abinci, amma ni ba wata aljana da na kira duk karyane". Ji yayi an sakar mashi riga, yana juyawa baya sai ya ga aljanar ta bace bat, ai kuwa ya ruga da gudu ya nufi kofar falo da nufin ya fita ya tsere. Ya kai hannunsa jikin kofar da nufin budewa, sai ji yayi an kama kanshi an daga sama, gaba daya ganganar jikinsa ta rabu da kasa, nan fa ya kwalla wani uban ihu, yayin da yake harharba kafafunsa dake cikin iska.
Murja, Saratu da Ummi dake bangaren baki suna karatu da gudu suka fito suna tambaya ko lafiya, domin sun ji ihun farko sun zata ma ba'a gidan bane. Hajiya Lami ta bisu da kallon banza bata ce da su kala ba. Ganin anyi banza da su suma basu sake yin magana ba suka tsaya gefe suna kallon ikon Allah. Su dai suna jin mutum yana ihu yana fadin a taimaka masa, amma sunga su Hajiya Lami sai washe baki suke suna farin ciki. Murja ta ce, "To shi dama wannan mutumi mai kamar boka kawo shi gidan sukayi don su sa karti su dakeshi ko kuwa". Saratu ta ce, "To wannan lamari Allah kadai ya san me ke faruwa". Naziru mai aljannu kuwa bayan shawagi da akayi da shi a cikin falon sai ji yayi an sako shi ya fado kasa da karfi. Nan take ya rike kugu domin yaji ciwon fadowar. Yunkurawa yayi ya tashi da nufin ya sake rugawa, yana cikin gudu kafin ya kai kofa ya ji an zura masa bulala ana fadin, "Koma ka dauki jakarka, da tarkacenka". Ba shiri yayi kwana ya juya yana sosa baya domin bulalar na shigarsa. Layoyin ya tattara duk da haka ana tsula masa bulala ya zuba su a cikin jaka ya kama hannun jakar tashi da nufin ya dagata ai kuwa sai yaji bala'in nauyi, tamkar ya daga buhun masara ko kuma wani katon dutse.
Ji yayi an kyalkyale da dariya wacce ta cika dakin, daga bisani yaji ance dauki mana ka bar gidan nan. Kuka ya fashe da shi domin yayi iya kokarinsa amma ya kasa daga jakar, "Daga cikin jakar ka fiddo min kaina dake ciki ka ajiye ni a kan kujera sannan ka tafi". Abinda ya ji an fada kenan cikin wata katuwar murya mai amsa amo. A dan tsorace yana zubda hawaye ya fara kokarin bude jakar tashi, tun a lokacin ya fara nadamar shiga harkar bokanci domin yau yasan Allah ne kadai zai ceceshi daga hannun wadannan aljannu. Yana bude jakar yaja baya da sauri saboda ganin kan aljanar da ya fara gani a cikin jakar ta kwalalo masa idanu sannan ta bude hakora tana mishi dariya. Ji yayi an talle keyarsa daga inda yaja baya ance, "Maza ka ciro min kaina mana". A matukar tsorace yake don shi a rayuwarshi bai taba shiga irin wannan halin ba. Jin da yayi ana ta marinsa a keya kuma ya duba baya ganin hannun da ke marinsa balle ya ga mahalukin dake marinsa, don dole ya je ya bude jakar ya sa hannayensa biyu dake karkarwa cikin jikar ya kamo kan ya fito da shi daga cikin jaka. Ji yayi kan ya ce, "Bi ni a hankali idan ka yarda ka kayar da ni sai na lahira ya fika jin dadi". Bai ce komai ba bayan ga hawayen dake zuba a idanunsa, jikinsa duk rawa yake, yana kyautata zaton da za'a tsaga jikinsa a wannan lokacin ba lalai a sama jini ba saboda tsoron da yake ciki. Karan gudu yaji a bayanshi, yana waigawa yaga gangar jikin mutum ce ta nufo shi a guje. Ai kuwa ba shiri ya saki kan ya runtuma a guje. Ji yayi ance, "Wayyo kaina, wayyo kaina. Kan nawa ka yar a kasa?"........................
Kuma dare yayi 🤭
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍