ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 52


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/3JCxKvOVecs
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-52-hausa.html


*^ Part52 ^*


Yana cikin gudu a falon ba zato ba tsamanni sai ji yayi charaf an chafke masa wuya, kasancewar falon akwai dan duhu, ko da ya kai dubansa da kai ga wanda ya rike masa wuyan sai ya ga ba kowa bane face ganganar jikin wannan matar wacce babu kai a jiki. Wani irin ihu ya kwala lokaci daya kuma ya sulale a kasa sumamme. Bayan dan lokaci, a hankali ya bude idanunsa ya kai dubansa fankar dake juyawa a saman falon, cikin dan kankanin lokaci abinda ya faru da shi ya fara dawo masa a kwakwala. Yana iya tuna yana zaune a rufarsa inda yake ba mutane magani da kuma bata hayaki ko turaren aljannu, Sailuba ta je wajensa ta ce masa kwatancen wajenshi akayi mata, nan har ta fada masa ga matsalarta cewa aljannu ne suka addabi gidan wata Hajiya. Jin ta ce Hajiya baiyi wata-wata ba ya fara karanto mata labaran karya da gaskiya na irin fafutuka da gwagwarmaya da yayi da aljannu, har ce mata yake yana juya aljannu kamar waina domin aljannu da sunji sunanshi har sakin fitsari suke a wando. Haka zalika a cikin kankanin lokaci kwakwalwarshi ta tariyo mai lokacin da suka sauka daga kan napep har masu gadi suka hanasu shigowa gidan, inda shi kuma yayi amfani da rufa ido da yan tsubbace-tsubbacenshi ya kunna wuta wacce a gefe ya kunnata su kuma suke ganin tamkar a kan kanshi wutar take ci. Ya san cewa hakan da yayi ba karamin kara samun yarda da aminci yayi a wajen su Hajiya ba. Haka zalika yadda yayi amfani da rufa ido yasa kyalle ya mike tsaye tamkar mutum, yayi karyar itace aljanar da ta addabi gidan har ma yake ikirarin cewa tana masa magana yana fada musu abinda tace. Alhalin kuma a zahiri shi ya sani ko a mafarki bai taba ganin aljani ido da ido ba ko da kuwa a suffar mutane ce, amma in ya kintata dai-dai matar da ya ga ta fito daga cikin kyallen nashi babu shakka aljana ce. 


Ko kadan bai manta yadda sukayi da ita ba, daga karshe ya san cewa ya ciro kanta daga cikin jaka ya ga gangar jikinta ta biyo shi da gudu hakan yasa ya yadda kan ya ruga da gudu, yayin da ya ji an shaki wuyansa da hannu ana kokarin daga shi sama, a lokacin da ya juya sai ya ga ba kowa bane ya shake masa wuya face gangar jikin wannan aljana da ta biyo shi, tun daga nan bai kuma sanin a wane hali yake ba sai yanzu da ya bude ido. A hankali ya fara waige-waige na gefe-da-gefenshi daga kwancen da yake. Tabbas ya gane inda yake har yanzu dai a cikin falon gidan hajiyar da ya zo fitarwa aljana yake. Ganin bai ga kowa ba a cikin falon hakan yasa ya tashi zaune. Yana sosa bayanshi da yake jin radadi saboda bulalar da ya sha dazu. "Sannu da tashi malam boka". Abinda ya ji an fada kenan daga bayanshi, lokaci guda yaji zufa ta jika shi sharkaf, a hankali ya juya domin ganin mai magana duk da yaji muryar macece. Wata irin firgita yayi hade da kwala ihu yaja baya, ita ce dai aljanar da kanta ya cire yanzu kuma ya koma kan gangar jikinta, zaune take a kan kujera ta sashi gaba tana yi masa murmushi wanda yake karawa jagulalliyar fuskar tata ban tsoro. "Shiiiit! Rufe min baki". Ta fada yayin da ta dalla masa harara. Ba shiri ya dakata daga ihun da yake ya sa hannayensa bibiyu ya matse bakinsa, duk jikinsa karkarwa yake, a rayuwarsa bai taba shiga bala'i irin wannan ba, bai ma san cewa haka aikin bokanci yake da hadari ba. Duk da kasancewar yayi shekaru da dama a cikin harkar bokanci, amma bai taba ganin abun tsoro makamancin wannan aljana ba. An dai sha kai mishi mutane kala-kala domin ya cire musu aljani ko kuma yayi musu magana. Wanda mafi yawancinsu maganin bacci kawai yake dora musu, wasu kuma ya hada kayan maye ya hayaka musu wansa suka fi karfin kansu, idan abun yayi musu yawa sai haukan nasu ya lafa a biyashi kudinsa shi kuma yaje ya sha shagalinsa. Ko a wannan karon ba dan wannan hatsabibiyar aljanar ta bayyana ba da tuni ya ci kudin su Hajiya Lami ya kama gabansa, tunda tuni ya saka musu yarda da shi a ransu. 


"Kai kalle ni nan, me yasa kake tsorona bayan kuma zuwa kayi ka fitar da ni?". Abinda ya ji ta fada kenan, wanda ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula. Maganarsa na karkarwa ya ce, "Wallahi dama karya nake ba babu wani aljani da zan fitar. Aikina ya fi kama da damfara, kawai in yi wa mutum yan dabaru na rufa ido in sa ya yarda dani daga karshe ya biyani kudaden aikina amma na rantse miki da Allah ban taba fidda aljani daga wani gida ba". Dariya yaji ta bushe da ita, ta dan jima tana yi sannan ta ce, "Lalai ka cika dan rainin hankali, da farko na zata kai bokan gaske ne, ashe kai kawai dan iskan, miye dalilin da yasa ka dauki wannan hakar a matsayin sana'a?". Da sauri ya ce, "Wallahi mutuwar zuciya ce kawai ba wani abu ba". "Babu duka babu zagi, sharadi daya zan gindaya ma daga yau ka tattara duk kayan tsafinka da rufa idonka ka toyasu ka kama sana'a". A zuciya yake tunanin, wane irin ba duka ba zagi bayan duk jikinshi kaikayi yake yi, kai ko tsoron da ta bashi yanayin bugun zuciyarsa ya canza ai shima wani abu ne makamancin duka. "Kaji abinda na fada ma". Ta fada da karfi, sai da ya zabura da sauri ya ce, "Na ji, kuma na rantse miki ko baki fada ba dama daga yau na daina wannan sana'ar domin ni na ga abinda na gani". Bata rai tayi hade da cewa, "Zuwa yanzu kasan cewa ni ba mutum bace aljana ce ko? Kuma kasan cewa ko bangwan duniya zakaje ba zaka tsere min ba a matsayinka na dan adam, don haka kar ma tunanin zaka yi min karya ya fado ranka. Domin yanzu dukanka kawai nayi, amma idan kayi min karya wato kaki daina sana'ar nan, to kashe ka zanyi har lahira, domin irinku basu da wani amfani a cikin al'uma". Cikin hanzari ya ce, "Wallahi na daina ko yanzu ma ga kayan nan zan bar miki ki toyasu duka, ni in dai zaki barni da raina bani da korafi a kan kayan". 


Murmushi tayi, wanda ya sa yayi saurin kauda kai daga barin kallonta, sannan ta ce, "Ai babu abinda zanyi da kayanka, yanzu ma tashi zakayi ka dauki kayanka da su zaka fita. Kuma ina gargadinka da ko alama karka nuna cewa mun hadu, ka nunawa su Hajiya artabu kuka sha da aljannun ka koresu gaba daya, ka tsaya ta biya ka kudinka sannan ka fita ka bar gidan nan". "To". Ya fada ba musu ya tashi ya dauki jakarshi ya nufi kofa da gudu-gudu sauri-sauri. Da yaje bakin kofar gani yake kamar aljanar na biye da shi zata sake jawi shi baya don haka da gudu ya kama kofar yaja, cikin sa'a kuwa ta bude. Suna tsatssaye a kofar falon, cikin murna da farin cikin za'a cire musu aljannu suka ganshi ya fito daga falon a guje kamar wanda aka koroshi. Saura kadan ya bankade Mama Dije dake saitin kofar ba don yayi gaggawar jan birki ba. Kallo ya bisu da shi daya bayan daya, yayin da suma shi suke kallo dauke da tambayoyi a bakunansu. Shi kuwa tunani yake a ranshi, wato ashe ma suna nan tsaye a kusa da falon suna jin yana ihu amma aka rasa wanda zai kawo masa dauki, ko uwar me suke tunani oho, ya dai tabbata ihun da yake yi duk da kasancewar babban gida ne har mutanen dake wucewa a kan titi na iya juyowa domin gaba daya muryarsa yake budewa a yayin da yake ihun. "Naziru mai aljannu ya ake ciki? Muna fatan dai anyi nasara" . Sailuba ce ta watsa masa tambayar wacce ita ta katseshi daga tunanin da yake, kallonta yayi hade da tuna gargadin da aljanar tayi masa ya ce, "Wai baku ji ihu ba a cikin falon nan". "Munji mana, ihun karti muka rika ji kamar suna magiya suna baka hakuri". 


Murmushin yake yayi kana ya gyara tsayuwarsa ya ce, "Ai ba karamin taimako Allah yayi muku da ya sa kuka sameni ba. Domin bayan mun fara artabo da mamar aljannun da suka addabi gidan nan, ta ga zan hallakata sai ta kira yan uwa da danginta. Shine fa sukayi min taron dangi, amma duk da haka na hada su na ci ubansu duk ihun nan da kuke ji kala-kala na su ne, suna rokona suna cewa in barsu suna jin dadin zaman gidan nan, amma na bata rai na fatattake su, yanzu haka ba dawowa ba ko kallon kofar gidan nan ba zasu sake yi ba". Bayan jin dogon bayaninsa gaba daya fuskokinsu suka yalwata da murmushi, Sailuba ta ce, "Yauwa ai na fada muku dama yau kashin aljannun gida nan ya bushe tunda suka hadu da mai aljannu". Mama Dije cikin farin ciki ta ce, "Yauwa wallahi har hankalina ya kwanta, amma da aljannu sun cikawa mutane gida, ranar nan fa da dare ina shiga ban daki na ga mutum tsugunne a kan toilet, amma kafin inyi wani yunkuri na ga ya bace". Tsalle Jamsy ta yi hade da cewa, "Na fi kowa murna, yanzu shikenan babu aljanar da zata takura min na koyi karatun alqurani". Ta kalli Ummi dake gefe hade da watsa mata harara, "Ke kuma zanyi maganinki, dazun naga har kagara kikayi wai don na kasa hardace wata aya". Jinsu kawai yake yi sama-sama amma hankalinsa baya kansu, sai leka falo yake tamkar wanda ya manto wani abu a ciki, don gani yake kamar zai ga aljanar nan ta fito ta shaki wuyansa. Hajiya Lami ta lura da waigen da yake cikin falo don haka ta ce, "Mai aljannu ko kayi mantuwa ne a cikin falon?". Da sauri ya ce, "Aa Aa, wato ina kara dubawa lungu da sako ne domin in tabbatar aljanu basu ajiye muku wani mugun abu a cikin gida ba, kuma sauri nake zan tafi yanzu aljannu sun fada min ana can an hada layi ana jirana".


Yana gama fadin haka yayi gaba, "Mai aljannu dan jira in shiga in daukko ma mana". To ya fada ya tsaya, amma ba don son ranshi ba, domin shi Allah-Allah yake ya bar gidan, in da an biye ta tashi kudin ma da ya barsu tuni yanzu da ya dade da barin gidan. Bayan Hajiya Lami ta shiga daki ta fito ta damkawa Sailuba kudi da yawa ta ce ta kai wa Nazirun, ganin kudin da yawa ita kanta Sailuba kafin ta karasa gareshi, sai da ta zari wani abu a cikin kudin ganin ba mai kallonta. Tana bashi ya juya yayi gaba cikin sauri tana masa maganar ita ba yanzu zata tafi ba shi kuwa bai ma saurareta ba yayi gaba abunsa. Ummi ta kalli mamanta ta ce, "Mama anya wancan mutumin ba'a tsorace yake ba?". Saratu ta ce, "Wa ma ya sani gashi nan dai kamar a zabure yake, ni ji nayi ma kamar shine ke ihu a cikin falon, amma kinsan irin mutanen nan masu hudda da aljannu ba'a gane musu, wani lokacin sai ki gansu kamar mahaukata". Murja ta ce, "Allah ya kyauta". Suka bita da amin. 



Misalin karfe sha biyu da rabi na dare, a kishingide take a kan gadonta sai chat take da abokanta tana jijiga kai ga wakar da ta ke ji a jikin tv wanda ta bude kara sosai. Kamar kullum hankalinta a kwance, ga wani karin natsuwa da take ji idan ta tuna aikin da akayi musu a gidan ta zu na cire aljannu, sabanin daren jiya da yinin ranar da duk hankalinta in yayi dubu a tasheyake, a lokacin da ta tuno da aljanar da ta saka ta karatun dole. Amma yanzu dole ta cigaba da sheke ayarta kamar yadda ta saba, kuma ba zatayi karatun addinin ba. Dif! Taji kamar an dauke wuta karar tv da take raira waka ya dauke, amma da ta kai dubanta jikin tv sai ta ga mutanen da ke rawa a ciki suna ta yin abunsu. Hakan yasa ta dauki remote control ta kara volume sai da ta kaishi karshe amma dai shiru ba kara. Idonta a kan tv ta ga ta fara farfari kuma sai ta ga tv na daukewa yana kawowa. Bata shirya ba sai ji tayi karan sifiku ya cika mata kunne, da sauri ta sa hannunta ta toshe kunneta hade da tusa kanta a cikin bargo dake kan gadon. Zuwa can ta bude kunnenta a hankali, ta kalli tv wasa ake da remote ana kara volume ana ragewa, abinda yayi matukar bata mamaki kenan, domin ga remote din a gefenta tana kallo. Wani sabon tsoro ne ya ziyarci zuciyarta, cikin gaggawa ta tashi taje ta kashe tv din hakan bai gamsar da ita ba har sai da ta zare socket na tv din. Juyawarta bata fi tako biyu ba domin komawa gadonta, taji wata murya mai kaushi ta ce, "Ke maza ki karanto min ayoyin da kika hardace yau, a karatun da na ce ki dinga zuwa kina koya wajen Ummi". Suman tsaye tayi ta kame a wajen, ba shakka ta tabbata murjar daga cikin speak na tv dinta yake fitowa, ga haske ta gani alamar tv din ta kunnu...............



Ayi maleji, ni dai nayi nann 🏃‍♂️


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments