*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IlTXhzD_Byw
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-54-hausa.html
*^ Part54 ^*
Su dai sun tabbata basu bar wani a cikin motar ba, ba tare da wani fargaba ba suka leka don ganin mai magana, abun yayi matukar daure musu kai ganin babu kowa a cikin motar. Hakan ta sa kai tsaye suka shiga motar, Khalil na kokarin tayar da motar ya ce, "Junaid wai ni kadai ne naji kamar anyi magana a cikin motar nan yanzu?". Idanunsa na lumshewa ya ce, "Nima fa kamar naji magana, amma da alamu kunnuwanmu ne kawai suka jiyo hakan". A gaban motar suke a zaune baki dayansu, yayi wa motar key kenan da nufin tafiya sai ji yayi ana kwankwasa glass din motar, sauke glass din yayi ya kalli mai kwankwasawa, kallo daya yayi mata ya kauda kai da sauri, wata tsohuwa ce mai wata irin tababbiyar fuska, hannunta rike da wani abu a leda sai ci take, mike masa tayi hade da cewa "Dan saurayi ga gyada". Cikin tsawa ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Ba za'a ci ba, dallah gafara kar na tureki da mota". Junaid ma da ya kalli matar ya runtse idonsa bai sake budewa ba sai da yaji Khalil ya ja motar yayi gaba, "Kai narantse da Allah da na ga matar can sai da na tsorata, ai na zata aljana ce". Khalil yayi dariya hade da cewa, "Banza motsaraci, wane irin aljana kuma? Kawai tsabar talauci da yunwa ne yake canzawa talakawa kama, shiyasa wasu in ka kallesu sai kaji sun baka tsoro". Junaid ya ce, "Wato kai baka yarda akwai aljannu ba ma kenan". "Eh din ban yarda ba, kwana biyun nan ma na ga su Mom dina sun tarki wani abu, duk sun sa tsoro a ransu, sai su rika firgita kansu suna fadin wai sunga alja... ". Shiru yayi yana kara zare idonsa da kyau domin tabbatar da abinda yake ganin daga cikin dan karamin madubin da yake a gaban mota domin ganin baya.
Mummunar matar mai matukar abun tsoro ce a zaune a kujerar baya ta motar, hankalinta kwance sai hambada gyada a baki take tana taunawa da bakakken hakoranta wanda duk sun dafe sunyi baki, ganin ya tsareta da kallo ta banka masa harara. Ai da sauri ya bar kallon madubin ya juya baya, amma sai ya ga wayam ba kowa a kujerar, ya duba ko wane gefe bai ganta ba don haka ya sake juyawa ya kalli madubin nan ma bai ganta ba. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida hankalinsa a kan tuki. Junaid ya ce, "Ya naji kana magana ka wani yi shiru". "Gani nayi maganar ma bata da amfani shiyasa kawai nayi na barta". Khalil ya fada yayin da ya cigaba da tukinsa hankali kwance. Yana cikin tafiya ne ya hangi wata mata cikin fararen kaya a kan titi tana daga masa hannu tamkar tana masa bye-bye. Tsuru ya bita da ido tabbas shi take kallo tun daga nesa har suka zo gittata. Sai da ya ga fuskarta ma tukun abun ya kara tsoratasa, idanunta jajaye fuskarta fari tass tamkar ta shafa hoda, ga bakin nata wani wargajeje.
Cikin faduwar gaba ya dubi Junaid hade da cewa, "Kai wai kana ganin abinda nake gani kuwa?". "Miye kake gani?". Ya tambayesa a takaice, "Wallahi wannan matar mai cin gyada na gani a cikin motarmu dazu, yanzu kuma na ga wata yar budurwa cikin fararen kaya a can tana daga min hannu". Dariya Junaid ya kyalkyale da ita hade da cewa, "Malam kwakwalwarka ce kawai take karanta maka banza-banza, an fadama kan yara gareka, babu wani g...". Tsit yayi yana kallon waje daya, tamkar dai yadda yaji Khalil din ya kwatanta masa shima haka ya ganta a saman wata bishiyar bedi tana daga masa hannu. "Khalil kalli can. Kalla Khalil". Ya fada da sauri yana nunawa Khalil bishiyar dake saitin glass dinsa ne. Ya kalli wajen da Junaid din ya nuna masa amma bai ga komai ba. "Ni fa banga komai ba, miye kake nuna min?". Khalil ya fada yayin da ya mayar da hankalinsa ga tukun da yake, "Wallahi kamar dai yadda ka fada min nima yanzu na ga wannan yar budurwar a saman bishiya tana daga min hannu". "Akwai matsala wallahi, to uban me mace zata fito tayi a cikin daren nan? Ni na sha kaiwa har karfe ukun dare a waje kuma in koma gida normal ba tare da na ga kowa a hanya ba, amma yau na rasa me yasa nake ganin mutane kala-kala". Haka suka cigaba da tafiya suna gane-ganen abubuwan tsoro kala-kala, wani in suka gani ma sai dai su rufe ido ko suyi gaggawar kauda kai. Tafiyar tasu da dan nisa kasancewar unguwar da suka je birthday na abokin nasu yana da dan nisa daga unguwarsu.
Tun daga nesa Junaid ya ce, "Kai Khalil me nake gani a can? Kamar mutanen fa a tsakiyar titi duk da fararen kaya kuma sun sa wani abu a gaba". Fitilolin sola na kan titi sun haske wajen fayau tabbas shima Khalil ya hango abinda Junaid din ya hanga. "Wallahi na gansu, mu canza hanya ne ko mu karasa?". Junaid ya ce, "To ai ba wani hanya sai wannan, idan muka ce zamu canza hanya tafiyar da zamu koma baya muyi ba kadan bane, kawai bi a hankali ka karasa wajen in mun ga abun ba mai yuyuwa bane sai mu juya". "To". Kawai Khalil ya fada yayin da ya rage gudun motar suka tafi a hankali, gaba daya kwayar da take kansu ta sakesu hankalinsu na kan titin, lokacin da suka kara kusantar wajen ba karamin mamaki abun ya basu ba. Mata suka gani ko wacce cikin farin mayafi wanda ya sauka har kasa, mayafin da ya fi kama da likkafani, sun saka makara a gaba sai kallon makarar suke suna kuka. "Junaid wallahi ba zan karasa wajen can ba, ban taba ganin irin abun nan ba, mata ne fa kuma kana ganin makara suka saka a gaba suna kuka". Junaid da shima tuni tsoro ya cika zuciyarsa ya ce, "Wallahi nima abun ya daure min kai, anya ba fatalwa bane, in na tuna wajennan akwai makabarta a kusa da yankin nan". Khalil yayi tsaki hade da cewa, "Kaji wani banzar magana, kawai dan ka gansu da farin abu a fuska sai kace fatalwa ne? Malama mutanene watakil matsafa ne kawai". Yana fadar haka ya fara kokarin juya motar domin yin kwana su koma baya.
Ya raba titin tsakiya da motar kenan yaji motar ta mutu, don haka ya fara kokarin tayar da ita amma taki tashi. Junaid na fadin yayi sauri ya tada ganin wata mata ta nufo gunsu da saurinta daga cikin jerin matan da suka sa makara gaba. Motar bata tashi ba har ta karaso, ya gane fuskarta sosai, matar da ya gani dazu ce mai katon baki fuskarta abun tsoro musamman yanayin fatarta da take fari fat tamkar ta bade jiki da hoda. Motar ta fara kwankwasawa, a hankali Khalil ya sauke Glass, "Ku saukko muje, ina zaku juya baku ga ana jana'izar gawa bane?". Kallon juna sukayi hade da zarewa juna ido. A zuciya suke tunanin kalaman matar, duk taron da suke hange babu namiji ko daya a ciki, to me ya hada mata da jana'izar gawa, bama wannan ba yanzu in angogon ya nuna musu dai-dai karfe biyu da wani abu na dare fa, tabbas akwai abinda yake tafiya ba dai-dai ba a cikin lamarin. Dukkansu tsoro ya fara shigarsu musamman idan suka kalli idanun matar da yake jawur kamar ba idon mutane ba. Bai ce mata kala ba ya cigaba da kokarin tayar da motar da yake ta key amma taki tashi. "Kai ku fito mana ya ina muku magana kuna kokarin tayar da mota?". A fusace Khalil ya ce, "Ba zamuje ba malama ki kama gabanki ki barmu da abinda yake damunmu". Daga tsayen da take hannu ta zura ta madubi ta falla masa mari hade da cewa, "Fito tun kafin raina ya baci". Ashar ya danna hade da cewa, "Ni kika mara?". Ai da rufe bakinsa yaji ta sake dalla masa mari.
Da sauri ya bude motar ya fito yana huce, cikin zafin nama ya daga hannu da nufin sheka mata mari itama, bisa mamaki sai ji yayi ya mari iska, ita kuwa tana tsaye a wajen ko matsawa batayi ba. Wani marin ya sake kai mata domin a na farkon yana tunanin ko gocewa tayi, kamar dai dazun iska ya ji ya mara bayan kuma idanunsa na kanta ya gani sarai bata matsa ba. Hannu ta sake dagawa ta sheka masa mari, dafe kunci yayi zuciyarsa ta fara karanto masa abubuwa da dama. Duk lissafinsa ya tsaya cik, ko ya yarda ko kar ya yarda yau fa yayi karo da aljana ko kuma fatalwa. Don haka wani masifaffen tsoro ya kamashi, muje na ce muku. Ba shiri ya fara tafiya jikinsa na karkarwa, Junaid ma da ya fito daga motar da niyar cin uban matar ya fito, amma ganin abinda ya faru yayin da Khalil ya kai mata mari yasa yayi saranda ya kame a waje guda. Binta sukayi a baya suna tafe suna karkarwa cike da tsoro, su ba abin su ruga a guje ba sun tabbata ba zasu tserewa aljani ko fatalwa ba. Lokacin da sukaje saitin wajen makara da matan suka sa a gaba suna kuka, Khalil ya leka cikin makarar abinda ya gani ne yasa ya ja baya a matukar tsorace bayan ya fasa ihu.............
Na baku izinin cewa yayi kadan, banma yi tunanin zan iya post yau ba saboda abubuwan da sukayi yawa, amma dan kar ace nayi fushi na rashin comments ne, jiya kam na ga bambanci da alamu korafina ya karbi gareku wasu sun yanke shawarar zasu rika comment din ko da da Thanks ne. 🥱
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍