*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/e0CWjiZhO6Q
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-55-hausa.html
*^ Part55 ^*
Ba komai ya gani ba face wata mummunar mata mai fuska a kwararrabe, idanunta sun zazzaro, duk da kasancewar an lulube jikinta yakr da farin mayafi, amma kuma sun bar mata kai a waje, haka zalika a rairan take kwance a cikin makarar. Lokacin da ya leka gani yayi tayi masa murnushi abinda ya kara tsorata shi kenan, mutumin da ake shirin yiwa jana'iza mai ya kai shi bude ido harda yiwa wani murmushi. Zai ruga wata daga cikin matan ta daka masa tsawa, ba shiri ya dawo ya hau layi. Jere suke sun zagaye makarar dake tsakiyar titi sai kuka suke suna zubar da hawaye, Junaid da Khalil Allah kadai yasan irin tsananin tsoron da ke cikin zukatansu, har a lokacin roko suke Allah yasa abinda ke faruwa mafarki ne ba zahiri ba. Ji sukayi an tattali kansu hade da fadin, "Kuyi kukan mutuwa dan ubanku kuma". Junaid ya kalli wacce ta dakesa a keya yayi saurin kauda kai don fuskar ba kyan kallo. A zuciyarsa yake nanatawa "Muyi kuka kuma?". Layi layi matan suka fara bi duk wacce ta zo sai ta lafta musu duka hade da cewa suyi kuka. Ganin irin dukan da suke sha, ga kuma halin da suke ciki ko shi ya isa ya sasu kuka ba sai an sakasu na dole ba. Hakan yasa suka rushe da kuka da hawaye, da faruwar haka kuma sai suka ji matan sun bushe da dariya, kallon juna sukayi abun duniya ya kara sha musu kai hakan yasa suka kara rushewa da wani sabon kukan wiwi.
Sun dan jima suna yi wata ta daka musu tsawa hade da cewa, "Kai kuyi mana shiru, ku tashi mu dauki gawar muje a kaita gidanta na gaskiya". Shiru sukayi suna zare ido, matar ta sa Khalil ya kama gefe daya na jikin makara, Junaid ma ya rike dayan gefen sannan wasu daga cikinsu suka rike sauran wajen rikewa a makarar suka nufi makabarta. Duk jikinsu karkarwa yake saboda tsoro, gashi lokacin da suka bar bakin titi suka nufi makabartar hanyar duhu sai su rika jin kamar ana shafasu ta baya sai sun juya su ga ba kowa kusa da su, wani lokacin kuma su rika jin kuka kamar na jarirai a gefen hanya. Ga makarar da shegen nauyi, tafiya mai dan nisa sukayi suka karasa makabartar kasancewar duk da security light makabartar ko ina a ciki haske fayau. Gefen wani kabari sukaje suka ajiye gawar a gefe, bisa mamaki sai gani sukayi wata mata ta miko musu diga ta tona rami da cebur wai su gina ramin kabarin. Junaid da Khalil suka kalli juna, su fa a tarihin rayuwarsu basu taba zuwa makabarta ba, saboda suna tsoron mutuwa yasa ko makabartar ma tsoron shigarta suke, yau gasu sune tsamo-tsamo a cikin makabarta kuma wasu mutane masu kama da fatalwa zagaye da su, bama wannan ba ta ina zasu fara gina kabari abinda basu iya ba?. "Wallahi ban iya gina kabari ba, a waya kawai na taba ganin yadda kabari yake". Cikin tsawa wata mata ta ce, "To yau zaka iya dan gidanku, maza ku fara".
Ba yadda suka iya haka suka fara tona ramin kabarin, sun sha bakar wuya domin suna yi matan na zafga musu bulala idan sun tsaya ko kuma sunyi kuskure a wajen ginin ramin. Bayan sun gama aka daukki gawar wanda su ganinta suke da ranta don har murmushi take musu ga kuma kwala-kwalan idanunta da take motsawa, aka sata cikin kabarin aka binne. Za'a tafi kenan suka ga matan na tattare mayafinsu daga kasa abinda suka kasa ganewa kenan. Wata daga cikinsu ta ce, "Sanin kowa ne a cikinmu idan anyi mutuwa an binne gawar tana dawowa duniya domin farautar mutane, duk wanda ta kama zata kasheshi. Don haka kowa yayi shirin ceton ransa duk wanda baya da gudu to yau sunansa gawa". Da fadar haka su Khalil suka ga matan nan na zafgawa a guje, ba shiri suma suka ara a na kare suka rufa musu baya. Suna cikin gudu sun nufi hanyar fita daga makabarta, kamar ance Khalil ya juya ya kalli baya, ai kuwa idanunsa suka gane masa hannu ya hudo kasar kabarin matar da suka binne. Cikin gudu yace, "Junaid kalli baya, wallahi matar da muka binne ce zata fito". Junaid da a matukar tsorace yake tuni zufa ta jika jikinsa don ko kadan baya son mutuwa ya juya baya. Lokacin kuwa ya ga kan matar ya fito daga cikin kasa, take ta aika masa wani irin kallo mai ban tsoro kanta da fuskarta duk cike da kasa. Wani ihu ya kwala hade da juyawa ya kara karfin gudunsa saura kadan ya fadi.
Sunyi gudu sosai bayan sun fita daga makabartar sannan suka juyo baya suka kalli kofar fita daga makabartar ai kuwa suka ga wannan matar ta fito a guje, yanayin kasar da ke jikinta duk ya kara mata muni bayan wanda take da shi. A irin gudun da take sun tabbata ba tare da bata lokaci ba zata tarar da su, gashi kuma su ta biyu kai tsaye, ko da yake suna fitowa daga makabartar suka nemi sauran matan sama ko kasa suka rasa. A cikin gudun da suke kowa ya kama gabansa suka shiga cikin lunguna suna sheka gudu. Ganin abun yake kamar a mafarki wai fatalwa ce take biye da shi a baya, abinda ko kadan bai ma yarda da shi ba yau gashi yana gani da idanunsa, abu na neman rayuwarsa. Lungu ya gani a kofar wani gida don haka ya shige hade da tsugunnawa ya rike bakinsa don ma kar yayi sauti wanda matar zata ji. Yana tsugunne yaga wani bakin abu ya wuce ta lungun a guje, shi dai kara dukewa yayi yana rike bakinsa. Ya dan jima a wajen har yayi niyar fitowa ya tsere, tunda ya ga abun ya wuce wanda yake tunanin matar ce. Sai kawai ya ga abu a gabanshi, d'aga kai yayi a hankali cikin tsoro domin ganin minene. Ihu ya kwala hade da tashi ya runtuma a guje, matar ce a tsaye ta bude hakora tana kokarin miko zankala-zankalan hannayenta zata kama shi.
Haka suka rika gudu cikin unguwa suna ihu, sun sha bakar wahala sosai domin duk inda suka nufa sai su ga abun tsoro, wani lokacin su ga jaki ba kai, wani sa'an su ga doki nayi musu dariya. Wani lokacin kuma su rika ganin matar ta nufesu da wuka tana shirin kashesu. Ihun da suke sa da ya tada yan unguwa marar tsoro daga cikinsu suka rika fitowa, masu tsoro kuma suka kara saka kubobi a dakunansu. Daga karshe mutanene suka ririke su Khalil wanda su kuma gani suke kamar wadannan matan ne suka rikesu, don haka suka rika kokarin kwace kansu suna ihu. Ganin kamar ba lafiya lau suke ba yasa mutane suka mika su ga ofishin yan sanda kafin safiya. Tunda safe da ta tashi take jaraba, ta hana kowa sukuni a cikin gida, yanzu ma waya take tana ta masifa "Bai dawo gida ba wallahi, yanzu haka a can wajen tsinannun abokan nasa ya kwana". Daga can ya ja tsaki hade da cewa, "Hajiya ai shiyasa nake ce miki ki daina barin yaran nan fitar dare, amma sai ki ce wai ai lokacinsu ne a barsu su ci duniyarsu wai wataran ba zasuyi ba. Ni dama abinda nake tsoro yanda yake ciko daren nan kar wani abu ya sameshi a hanya". "Kaga Lawal karka bata min rai mana, ya na kiraka ina fadama damuwana kai kuma kana mun wata maganar daban, to tunda yaran suke fitar dare ka taba ganin wani abu makamancin haka ya faru ne?". Daga can ya ce, "Yau kuma Lawal ma kai tsaye babu baban Khalil din kenan". "Ai kai ne da abun haushi wallahi". "Yi hakuri Hajiya uwar gida ran gida, yanzu miye abun yi?". Zatayi magana kenan ta ji kiran Khalil din ya fado wayarta , don haka ta katse wayan da suke ta dauki kiran. Daukar farko da tayi har ta fara fadin, "Gidan ubanwa ka kwana? Ba na fadama ka daina kwana a gidan abokai ba?". Sai ta ji ana cewa, "Assalamu alaikum, barka da safiya, don Allah idan da mahaifiyar mai wayar muke magana muna bukatar ganinta a police din gangaren Nufawa".
"Police kuma? Me ya kai Khalil police kuma malam?". Daga can ta ji ance, "Maganar ba zata yuyu a waya ba, sai kun zo". Yana fadar haka ya kashe wayar, Mama Dije ta kalleta hade da cewa, "Naji kina ambatar police me ya faru ne?". Kallon Jamsy Hajiya Lami tayi hade da cewa, "Ke yi sauri ki daukko min gyale na". Sannan ta juya ga Mama Dije ta ce, "Khalil ne wai yana station din Gangaren Nufawa, watakil rikicin nasu ne sukayi da abokai wanda suka saba, bari naje na karbo sa". Mama Dije ta ce, "To ai ina ganin ba sai kinje ba kawai ki kira dpo din mana". "Bari dai naje naji wanda ya kira din yace da bukatar inje". Bayan Jamsy ta kai mata gyale suka fita da driver. Suna zuwa police din aka shaida mata ai su Khalil na asibiti shi da abokinsa sai zare-zare suke suna fadin gata nan- ga ta nan. Likitocin sun tabbatar yana shaye-shaye, ita kuwa ta ce ba wani shaye-shaye aljannu ne kawai ko mayu suke neman hallaka mata danta. Kusan wuni tayi a asibiti, ita da iyayen Junaid daga karshe bacci ne ya kwashe su Khalil bayan sun farka ne suka fara dawowa hayyacinsu. Sun yiwa iyayen nasu bayani, tun daga kan matar farko da tayi musu magana har zuwa kan binne gawa da sukayi. Iyayen Junaid dake yan boko ne ciki da bai suka ce watakil dai kanshi ne ya fara tabuwa domin labarin da suka bada sam abun ko a mafarki ba zai yuyu ba.
A bangaren Hajiya Lami kuwa ta yadda da labarin domin ita duk abinda akace da aljani to tasan komai na iya faruwa. Musamman yanda ta ga jikinsu duk an sa musu bandeji saboda rauni da sukaji wajen gudun tserewa aljana kamar yanda suka fada. Daga karshe bayan likita ya shaida musu ba wata damuwa kowa ya dauki dansa yayi gida da shi, motar Khalil ma sai daga baya driver ya koma ya daukko ta. Bayan kwana biyu Khalil na gida yana jinya amma baya da labari sai labarin aljannu, kullum a tsorace yake, ko kyankyaso ya gani sai ya zabura. A bangaren su Hajiya Lami kuwa damuwarsu daya sun kasa samun damar daukar hoton Murja. Zaune suke a falo kowa na sha'aninsa, Murja ta zo wucewa zataje wajen su Saratu ta dan russuna ta gaishe da Mama Dije da Hajiya Lami. Babu wanda ya amsa a cikinsu sai kallon banza da suka bita da shi, ba'a fi minti biyu da wucewarta suka sake ganin Murja ta fito daga bangarensu, kai tsaye taje ta zauna a daya daga cikin kujerun falon tana hararansu. Gaba daya kawunansu sun kulle, sun ga Murja ta fita amma basu ga dawowarta cikin falon ba sai gashi ta sake fito daga dakinsu a karo na biyu.
Suna zaune Jamsy ta tashi sume-sume ta fita waje, kai tsaye bangaren su Saratu ta nufa kwakwalwarta na zayyano mata abubuwa da dama, tana zuwa ta fada falon ko sallama babu. Murja ta gani a zaune suna kallo a tv suna ta dariya. "Wallahi Murja guda biyu ne". Ta fita a guje tana fadin, "Mom! Mom zo ki ga Murja guda biyu ce". Su Saratu kallo kawai suka bita da shi basu fahimci abinda take nufi ba. Tana zuwa ta ga dayan Murja zaune a falon nasu, cikin tsoro ta ce, "Mom wallahi Murja guda biyu ce, ga daya a nan kuma ga daya a can falon baki wajen su Saratu". Mikewa tsaye Hajiya Lami da Mama Dije sukayi, "Murja guda biyu kuma? Taya haka zai yuyu?". Murja ma ta mike tsaye tana kallon Jamsy, "Wane irin na zama guda biyu kuma?". Basu ce da ita kala ba suka fita daga falon da sauri domin zuwa su gano dayar Murjar, ai kuwa itama Murja ta bi bayansu. Tsaye sukayi suna karewa juna kallo, su kansu yan cikin falon harda su Saratu sakin baki sukayi suna kallon Murjojin guda biyu, hatta kayan jikinsu iri daya ne. "Baiwar Allah wacece ke?". Murja ta fada, yayin da dayar ma ta ce, "Ni ce Murja ke dai wacece ke?"...................
🤔 Bana son hayaniya, in kun gano Murjar a cikinku sai mu cigaba
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍