ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 56


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/gwnNqikbThg

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-56-hausa.html


*^ Part56 ^*



Murjar ta gaskiya ta dubi Safuratu, wacce tana sane itace ba kowa ba zaiyi wannan abu hade da cewa, "Kowa yasan ni ce Murja, dan Allah ki fada mana ke wacece?". Nunata Safuratu tayi da yatsa hade da cewa, "Karku yarda da ita, ni ce Murja ta gaskiya, wannan bansan ko wacece ba". Idanu kawai suke binsu da shi suna kuma sauraran gardamar da ta balle a tsakanin Murjojin biyu. Babu bambanci ko kadan a tare da su. Duk sun rikita kwakwalen mutanen da ke wajen. "Wallahi ni ce Murja ta gaskiya". "Karku yarda da ita ni ce nan Murja ta gaskiya". Hajiya Lami ta kallesu baki sake, "Kai kunga ku tsaya, da hankalinmu fa karku mayar da mu mahaukata mana. Aa kamar ya Murja guda biyu, cikinku wacece Murjar wacece kuma ba Murja ba? Kuma ya akayi wacce ba Murja ba ta zama Murja?". Mama Dije ta ce, "Haba! Haba! Ai ni tun ranar da yarinyar nan ta zo gidan nan ta ce wai itace Murja na san cewa karya take, kawai dai akwai wata a kasa amma Murja ta dade da mutuwa, watakil aljannu ne kawai suke mana wasa da hankali". Hannun Mama Dije Safuratu ta kama hade da cewa, "Mama Dije kema shaida ce ni ce Murja ta gaskiya". Da sauri Mama Dije ta warce hannunta hade da cewa, "A gidan ubanwa nake shaida din? Ni wallahi dukanku ban yarda da ku ba". Murja ta gaskiya ta ce, "Wallahi ni mutum ce ba aljana ba kuma ni ce Murjar gaskiya". Tsaki Hajiya Lami tayi hade da yin hanyar waje tana fadin, "Yanzu zan sa a kira Naziru mai aljannu, idan ya zo ma gane wacece Murjar kuma wacece ba Murjar ba, idan kuma dukanku aljannu ne wallahi sawa zanyi ya toya ku". Waje tayi Mama Dije da Jamsy suka rufa mata baya itama Safuratu ta bi bayansu.


Suna fita Saratu ta kalli Murja cike da shakku a zuciya ta ce, "Me yake faruwa ne Murja? Ita waccan din wacece komai naku iri daya hatta Murya da kaya ba bambanci?". Murja ta ce, "Gata nan dai nima har yanzu abun mamaki yake bani, taya za'ayi haka dama ana samun wani mai kama da mutum komai da komai ne?". Ummi dake baya-baya da Murjar ta ce, "Ni fa Mama tsoron Murja ma nake ji, to ai har yanzu bamu san ko itace ta gaskiyar ba ko kuma ba ita bace". Murja tayi murmushi hade da cewa, "Ummi kwantar da hankalinki wallahi ni ce Murja". A bangaren Hajiya Lami kuwa tana zuwa ta sa Mama Dije ta kira Sailuba take fada mata abinda ya faru, don haka ta ce suyi gaggawar nemo musu Naziru mai aljannu. Ai kuwa Sailuba tana katse kiran ta kira Naziru mai aljannu. Tayi masa kira ya fi goma tukun ya dauka, tana ce masa aiki ne ya samu, yayi sauri ya kashe wayar. Da kyar ta sake samu ya daga wayar, nan yake ce mata shi fa ya dade da ajiye harkar cire aljannu yanzu haka ya koma tallar kankana a bakin titi. Mamaki ne ya cikata amma haka ta kashe wayarta ta kira Mama Dije ta sanar mata. Yayin da ita kuma Mama Dije ta ce a samo musu koma waye malami ne ko boka duk wanda ya samu. 


Bayan Bincike daga karshe dai Sailuba ta nemo musu wani ustaz mai rukiyya. Kai tsaye suka shiga gidan, aka kira Murjojin guda biyu aka zaunar da su a falo yayin da Malam ya sasu gaba yana kallonsu. Shi kanshi tunda ya zo duniya bai taba ganin abun mamaki kallar wannan ba. Yayi magana da su baki daya amma ko wacce ta ce itace ta gaskiya, don haka ya fara karatun rukiyya amma yaji shiru. Daga karshe ya fara yi musu barazanar zai toya aljanar cikinsu, hakan ma dai baiyi wani tasiri ba domin ko kadan bai ga alamun tsoro a idanun ko wacce ba. Yayi karatu a cikin ruwa ya watsawa ko wacce, sannan ya yi amfani da magungunansu irin na islamic kala-kala amma ya ga ko tari babu wacce tayi a cikinsu. Don haka daga karshe dai ya ce a cikin Murjojin guda biyu baya tunanin akwai aljana kuma baya tunanin akwai mai aljannu ma a cikinsu, domin irin abubuwan da yayi da akwai mai aljannu da tuni sun tashi. Hajiya Lami dai tana tsaki ta sallameshi ya tafi tana ta wa Sailuba masifa wai ai malamin nan bai iya komai ba watakil ma dan damfara ne kawai. Nan dai suka yanke shawarar a nemo musu boka ko yan bori. Sailuba bata sha wahala ba taje ta kwaso musu yan bori, suka zo suka tare a gidan suna ta haukansu na bori sunyi iya yinsu amma babu abunda daya daga cikin Murjojin sukayi sai ma dayar Murjar dake binsu da harara kamar zata dake su.


Suma dai haka Hajiya Lami ta sallamesu suka tafi bata daddara ba ta sa aka kira boka, kamar sauran shima ba biyan bukata, bayan yayi yan tsubbace-tsubbacensa a kan su Murja ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi Hajiya Lami da ta kwalala masa ido itama ya ce, "Wannan yan matan da kike gani dukannsu mutanene babu aljana a cikinsu. Domin da akwai aljana a ciki da tana ganina zata zura a guje ba zata tsaya ba sai taje bangon duniya". Hajiya Lami ta ce, "To ai ita yarinyar kowa yasan ita daya ce ba yan biyu bace ita din taya za'ayi yanzu kuma ta zama biyu". Nan fa boka yace ai irin haka ta sha faruwa nan ya rika kwaso labarai kala-kala yana ba ta wai na mutanen da suka zama yan biyunsu bayan sun girma. Gaba daya hankalinta bai dauki maganganunsa ba, haka dai ta sallameshi ya tafi. Dole ta sa suka hakura suka bar Murja biyu a gidan da tunanin daukar hotonsu gaba daya su kai wajen boka ya kashesu duka a huta tunda an kasa gane wacece Murja ta gaskiyar a cikinsu. Sai dai kwana biyu suna iya kokarinsu domin ganin sun dauki hoton murjojin guda biyu amma abu ya gagara. Kamar kullum yau zazzaune suke a falon sai hamma suke sakamakon bashin baccin da suka ci, dan kwana biyu suna kaiwa karfe biyu ko ukun dare duk suna hako domin samun damar daukar hoton Murja, sau da dama sai sun tunkari kofar sai suji alamun su Murja din a farke suke. 


Yau ma misalin karfe daya da rabi Hajiya Lami ta isa kofar dakin, ta dan dade a wajen amma ta ji shiru babu alamun motsin mutane. Cikin farin ciki ta karasa ta fadawa Mama Dije, don haka suka nufi dakin da sauri, dama da safaya key suke zuwa, idan ma sun tarar da dakin a kulle sai su saka makulli su bude. Safuratu na jinsu suna kokarin budewa, ai kuwa tayi saurin sa bargo ta lullube kan Murja, yayin da ita kuma ta kwanta rairan yanda zai basu damar daukar hotonta ba tare da wani matsala ba. Ai kuwa suna shiga ba karamin farin ciki sukayi ba bayan sun kunna wutar dakin sun ga dayar Murjar fuskarta na kallon sama duk da kasancewar basu san ko itace Murja ta asali ba. Daukar hotonta kawai sukayi, sannan suka koma gefen Murja suna kokarin daga mayafin domin daukar hotonta suka ji ta fara motsi, hakan yasa sukayi gaggawar fita daga dakin don kar ta tashi. Washe gari tun da safe suka kira Sailuba tayi musu jagora zuwa wajen Boka Kare Dangi, hoton ma a hanya suka wanke shi a wani shagon daukar hoto. Zaune suke suna ta zare idanu, yayin da shi kuma ya karbi hoton ya kyal-kyale da dariya, cikin muryarsa marar dadin saurare ya ce, "Ai wannan aiki ne mai sauki, domin kashe yarinyar ba zai bada wahala ba kasancewar dama aljana ta taba shiga cikin jikinta. Ina sa ran ma tsakar dare zan sa aljana Zilzillah ta je ta kasheta". Nan take farin ciki ya kama su Hajiya Lami. A nan suka bashi labarin yadda Murja ta zama guda biyu, tare da rokonsa idan zai yuyu a kashe su dukansu. Karsu sama damuwa ya ce yayin da suka ajiye masa kudi masu yawa suka yi bankwana suka koma gida cikin farin ciki, domin boka ya musu albishir da mutuwar Murjojin duk biyu.


Zaune take a falo ita kadai, hadari ya taso sai walkiya ake ga iska yana bugawa, babu wutar nepa amma sun tada generator kasancewar kusan ko da yaushe gidan baya rabuwa da wuta, idan ma babu nepa to zasu tayar da gen. Lokaci daya wutar dakin ta fara farfari yayin da kwayayen dakin suka rika kadawa tamkar zasu fado kasa, wani irin iska ne mai karfi ya rika shiga cikin falon, saboda karfinsa tamkar zai kwashe komai na falon. Safuratu dake jikin Murja zaune take ko gizau batayi ba, kamar dai yanda take tsammani tunda ta bari su Hajiya Lami suka dauki hotonta, kuma yau da safe ta ga sun tattara sun fita unguwa ta bisu a baya. Ko da ta ga sun nufi hanyar garin su Boka Kare Dangi ta san can suka je. Kuma tasan ba komai zai kaisu wajen Boka Kare Dangi ba face wani makirci irin nasu da suka saba kullawa. Yanzu ta gane dalilin da yasa suka shafe kwanaki suna neman hoton Murja, wato Boka zasu kaiwa, shi kuma yayi sihirin da ya saba ya turo aljannu domin su kashe Murja. Shiyasa ta kasa ta tsare, bata yarda ta raba jiki da Murjar ba ma don kar wani abu ya sameta. Wata dariya ta ji an kyalkyale da ita mai firgitarwa, cikin kankanin lokaci kuma sai ta ji an fara magana cikin muryar mace, muryar da ko kadan bata da dadin saurare, kai daga kaji muryar kasan cewa ko da ta kasance muryar aljani ne, amma aljannun ma irin shaidanun aljannu wanda babu fari a zuciyoyinsu sai baki.


"Gaske tunda na karbi aikin nan naji gabana yana faduwa, ashe wacce zan kashe tana tare da aljana mai bata kariya? Sai dai kash yar uwa a yau kin taki rashin sa'a da kikayi gamo dani, domin ni aljana Zilzillah a tarihina ba'a taba bani wani aiki wanda ya gagareni ba, wallau na kashewa ko na haukatarwa ko kuma na saka cuta, ina iya kwashe shekaru masu dama ina bibiyar dan Adam domin cika umarnin aikin da aka sani. Shiyasa bokaye da malaman tsubbu suke matukar jin dadin aiki dani". Safuratu tayi murmushi bayan jin dogon jawabin aljanar ta ce, "Ni dake ba'a san wacce ta hadu da mummunar sa'a ba, domin ni ko da yaushe ina tare da mai bada sa'a shine Allah, sabanin ke da kike tattare da shedan ko da yaushe kina cikin rashin sa'a. Sa'ar ki tana farawa ne kawai a yayin da mutumin da kike son cutarwa ya fita daga hanyar Allah ta tsarki ya shiga cikin wani sabon ubangijin". Da jin haka aljanar ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya wacce ta fi ta baya karfi da ban tsoro, cikin lokaci kankani wani bakin hayaki ya gauraye saman falon sannan ya rika dunkulewa waje daya, ba'a dade ba sai ga wata mummunar mata ta bayyana cikin bakakken kaya. Gashi ne busu-busu a jikinta duk ya rufe mata fuska. Haka zalika wani bakin hayaki na fita daga cikin kofofin gashinta. Tabbas aljana Zilzilla mummuna ce ta gaske kuma yanayin halittarta na da matukar ban tsoro, idan mutum ya kalli fuskarta yana iya zaucewa ya fita hayaccinsa saboda tsoro. Ko da ta gama bayyana sai ta kalli Safuratu sannan ta daka mata tsawa tana cewa, "Ina umartarki da kiyi gaggawar fita daga jikin wannan yarinyar domin yanzu zan kasheta, idan kuma ba haka ba zan hada har da ke in kashe". Dariya Safuratu ta kyalkyale da ita a karo na farko, sannan ta watsawa aljanar wani malalacin kallo cikin cewa, "Me yasa kike bata bakinki? Kiyi gaggawar kashe mu idan kuma kika kasa kasheni, ki sani ba zaki bar gidan nan a raye ba. Domin nayi alkawari idan har ina tare da Murja ba zan bari wani abu ya sameta ba, in kuwa kika ga wani aljani ko mutum yayi nasarar kasheta ina kusa to ki tabbata ni ya fara kashewa".


Da jin haka sai aljana Zilzilla ta fusata, nan take katoton kanta ya kama da wuta, yayin da ta kara muni da ban tsoro, ta bude wawakeken bakinta ta kurma uban ihu mai matukar rikitarwa, domin sai da iska ya kara cika dakin saboda karfin ihun nata. Da faruwar hakan hakoranta suka kara tsawo da kaifi, idan ka kalli bakin sai ka ga tamkar bakin damisa, cikin hakan tayi wani irin ruri mai matukar amo tare da kaiwa Murja cizo a wuya cikin saurinsu irin na aljannu. Sai dai kafin bakinta ya karasa wuyan Murja sai ji tayi an cafke mata wuya da hannu daya. Abinda yayi matukar bata mamaki kenan, batayi wata-wata ba, ta kaiwa Safuratu din yago da farcen hannunta domin ta raba wuyan Murja da gangar jikinta, ai kuwa da sauri Safuratu ta goce, sai dai farcen Zilzilla ya sama jikin habar Murja inda ya karci wajen nan take ya fara jini, ko da ganin haka sai ran Safuratu yayi matukar baci, don haka ta daga Zilzilla da hannu daya ta makata da kasa kuma ta sa kafarta ta taka mata wuya. A dai-dai lokacin babu irin yunkurin da Zilzilla batayi ba domin ta kwace kanta amma ta kasa, sai a lokacin ta fara nadama don ta gane cewa ko kusa karfinsu ba daya yake da na Safuratu ba, ta fita karfi nesa ba kusa ba. Safuratu kuwa hannu ta dunkule ta kaiwa Zilzilla wani wawaan naushi a fuska, nan take hancinta ya fashe wani irin bakin jini ya fara fita daga hancin.... .............


Kai aljannu idan kun gama fadan ku sanar min in cigaba da bada labarin, ni duk tsoro ma ya kamani, nayi nan 🏃‍♂️


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Comments