🧟♀️🧟♀️ 🧟♀️🧟♀️
*ALJANAR FATIMA BOOK 2*
🧟♀️🧟♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟♀️🧟♀️
By *Kingboy Isah*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/DT-uH4043IM
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-61-hausa.html
*Busy* 🥱
*^ Part 61 ^*
Hamza da Mubarak dake zaune suma mimmikewa sukayi tsaye hade da daga hannuwa sama suna kallon motane da basu wuce su shida ba, da alamu dai barayi ne domin cikinsu ko wanne rike yake da bindiga a hannu. Wani daga cikin barayin ya ce, "Ku bude mana gida, ku biyu ku tsaya ku yi gadinsu duk wanda ya motsa ku fasa mai kai, ku kuma ko zo mu shiga daga ciki". Ya dakawa Sunusi tsawa hade da ce, "Maza ka buda mana gidan nan, kuma a cikinku kar wanda ya yarda yayi mana ihu". Sunusi yana karkarwa ganin su hudu sun saita shi da kan bindiga ya sa yaje ya bude musu gidan. Ai kuwa suka fada cikin gidan, yayin da sauran barayin guda biyu suka tsare su Sunusi a waje da bindigogi. Harbe-harbe barayin suka fara yi tun daga tsakar gida, su Saratu suna daki suna bacci suka fara jin harbin bindiga, don haka a tsorace suka tashi ita da Ummi suna salati.
Kai tsaye barayin suka nufi babban falo na gidan cikin gudu-gudu sauri-sauri. Suna murda kofar sai gani sukayi ta bude don haka suka tsaya a tankamemen falon suna rarraba ido. Ogan nasu mai suna Jan Zaki ya kalli yaran nasa guda uku hade da cewa, "Kuyi gaggawa ku shiga lungu-da-sako na cikin gidan nan ku fiddo mutanen gidan". Da fadar haka su duka suka ce, "An gama oga". Nan take suka rarrabu wasu sukayi saman bene yayin da wasu suka nufi dakunan kasa suna duddubawa. Shi kuma ogan ya sama kujera ya zaune a babban falon yayin da ya zurawa tv ido da take ta faman karatu. A zuciya ya ce, "Lalai masu kudi yan iska ne, mu muna can muna fama da sauro gashi su wutar tayi musu yawa har tv ake bari a kunne". Daya daga cikin yaransa ne ya fito daga cikin kitchen yana lashe hannu. Jan Zaki ya kallesa hade da daka masa tsawa ya ce, "Kai Biri uban me kake ci? Kai da aka saka nemo mutanen gidan?". Wanda aka kira da suna Biri ya dan sosa keya hade da cewa, "Mai gida ai na zata wancan daki ne, to da na shiga sai na ga ashe kitchen ne. To a cikin wata tukunya sai na ga farfesun kaji shine na ciri cinya daya na dan maida mugun yawu".
Da jin ance kaji Jan Zaki ya fara hadiye yawu, ya ce wa Biri yayi sauri ya daukko masa tukunyar. Ba jimawa sai gashi ya daukko mai tukunyar ya direta a gabanshi. Kallon cikin tukunyar yayi, kaji ne manya wanda akayi farfesunsu, sai kamshi yake tashi. Hannu ya sa ya dau kaza daya ya cizgi cinya daya hade da kaiwa baki ya fara ci. Biri yayi tsaye yana kallonsa, ganin ogan nasa ya ki kulasa ma balle ya ce ya dauka shima, hakan yasa ya kai hannu da nufin ya dauki naman. Oga Jan Zaki ya bige hannun, bakinsa cike da nama ya ce, "Kai fa Biri shegen kwadayayye ne, aiki muka zo gidan nan ba zalama ba, don haka kayi gaggawar zuwa domin fito da mutane". Yana ji yana gani Jan Zaki ya hana shi daukar nama. Hanyar wasu dakuna ya nufa yana waigen baya, sai hadiyar yawu yake yanda ya ke hango Jan Zaki na kai naman kajin baki. Daki ya fara duka tamkar zai karya kofar dakin, su Murja na zazaune bayan karar bindiga ya tayar da su, sukaji ana buga kofa, irin dukan da ba na lafiya ba. Safuratu ce ta tashi tana fadin "Waye? Waye?". Daga can taji ance, "Bude ko na karya kofar nan". Tashi tayi ta nufi kofa domin bude kofar. Murja na zaune a gado tana kallonta, ta ce, "Safuratu waye a bakin kofar?". Safuratu ta ce, "Nima ban sani ba, naji kamar ba muryar dan gidan nan ba".
Dai-dai lokacin ta bude kofar, tana budewa ya turo da karfi hade da nunata da bindiga. Murja na ganin mutum da bindiga ta kwala uban ihu. Shi kuwa da sauri ya harba bindiga, hade da cewa, "Kuyi mun shiru, duk wacce ta kuskura tayi ihu sai na harbeta ta mutu, ku fito muje". A tsorace suka fita Biri na biye da su da bindiga a hannu. Sun kusan zuwa tsakiyar falon suka ga an fito da su Hajiya Lami gaba daya hannuwa a sama mutane biyu rike da bindigu suna binsu a baya. A falo suka zube gaban Jan Zaki da ke ta faman cin naman kaji yana lashe hannu. Bayan ya kallesu daya bayan daya, ya dauki bindiga hade da nuna Hajiya Lami da ita ya ce, "Ina kudi?". Hajiya Lami na karkarwa ta ce, "Wallahi babu kudi". Daya daga cikinsu ne ya daka mata tsawa hade da cewa, "Zan makeki da bindigar nan idan baku fiddo kudi ba". Mama Dije tana karkarwa ta ce, "Dan Allah kuyi hakuri, wallahi da gaske babu kudi cash a wajen mu, sai dai idan kuna son transfer ne". Dariya Jan Zaki ya kyalkyale da ita hade da cewa, "Transfer? Kin zata mu jahilai ne? Salon idan mun tafi ku bi didigi ku kama mu kenan?". Mama Lami tayi shiru, kallon yaran nashi yayi hade da cewa, "Kai maza ku shiga gidan nan ku bincike ko ina idan kunga kudi ko kayan kudi ku kwasosu". Da jin haka suka ce "An gama oga". Nan take suka warwatsu suna bincike gidan, shi kuwa Jan Zaki ya cigaba da cika bakinsa da naman yana fadin, "Idan babu kudi a gidan nan, na rantse da Allah garkuwa zamuyi da ku sai an biya kudin fansa".
Sun duba duk inda suke tunani basu samo kudi ba, Biri ne ya saukko daga sama rike da wata leda mai nauyi da alamu akwai wani abu a ciki. Hannunsa kuma rike yake da chocolate sai ci yake yana lumshe ido saboda dadinta. Jan Zaki na ganinshi rike da ledar ya washe baki hade da kallon sauran yaran nasa ya ce, "Ku dai malalata ne wallahi, a cikin gidan nan baku iya samo komai ba sai tarkacen sarkokin nan, wanda bamu da tabbacin ko masu tsada ne. Amma shi Biri yana hawa sama gashi har ya dawo da leda a hannu". Biri na karasawa wajen Jan Zaki ya kara fadada murmushin fuskarsa yana fadin, "Yauwa Biri kudin cikin ledar dollars ne ko Naira?". Kallonshi Biri yayi hade da zare ido ya kara kallon ledar dake hannunsa, zuwa can ya ce , "Oga wallahi ban samo komai ba a cikin gidan nan sai wannan chocolate din, a cikin ledar ma duk chocolate ne, na ce tunda bamu sama kudi ba bari mu daukko kayan kudi". Ran Jan Zaki ne ya baci, ya tashi a fusace hade da gaurawa Biri mari. "Kai dai wallahi Jaki ne Biri, kai kenan babu abinda ka sa gaba sai ciki? Wannan kajin ma fa kai ne ka lalubo su saboda shegen maita irin naka". Jan Zaki ya ajiye ledar mai dauke da chocolate hade da gyara rikon bindigarsa ya ce, "Tuba nake Oga". Tsaki Jan Zaki yayi ya kalli Hajiya Lami a fusace sannan ya wanka mata mari ya ce, "Wato ku yan iska bakwa ajiye kudi a cikin gida ko? To wallahi ba zamuyi zuwan banza ba, dole zanyi garkuwa da yayanki in ya so ku kawo min kudin fansa sannan ku karbe su". Jamsy da Murja ya kalla hade da daka musu tsawa ya ce, "Maza ku tashi da ku zanyi garkuwa". Da sauri Hajiya Lami ta ce, "Ranka ya dade dan fashi don Allah karka dauki wannan". Ta nuna Jamsy, "Ku hada wadannan biyun ku tafi da su kafin mu hada kudin". Ta nuna dayar Murja. Ya dube su hade da cewa, "Ok wato kin fi son wannan da kika ce kar mu dauka ko? To dan haka dole da ita zamu hada".
Da sauri Mama Dije ta ce, "Aa ranka ya dade Dan Fashi, ita wannan yarinya ce bata girma ba amma su wadannan sun girma sosai ayi mana alfarmar nan". Duban su Murja yayi sannan ya ce, "Wai ya nake ganinsu kala daya ne, har kayan jikinsu kala daya". Mama Dije ta ce, "Ai yan biyu ne, 'Ya'ya na ne a haka na haifo su suna matukar kama, shiyasa suke saka kaya kala daya". Biri ya kalleta hade da cewa, "Kin tabbata kina matukar sonsu?". Mama Dije ta ce, "Wallahi ina sonsu sosai". Dariya Jan Zaki yayi sannan ya ce, "To zamu tafi da su, kuma wallahi idan baku biya kudin fansarsu ba, zamu rika musu fyade na rashin imani har su mutu". Da jin haka Murja ta fashe da kuka, ta rike kafar Mama Dije tana fadin, "Dan Allah karki bari su tafi damu Mama Dije, kina ji fyade fa yake cewa". Cikin kukan karya Mama Dije ta ce, "Kiyi hakuri Murja ba zamu bari ki dade a hannunsu ba, goben nan zamu hada kudade mu karbo ku". Ririke Mama Dije Murja tayi tana kuka tana fadin karsu ba yan ta'adda su, Safuratu na ganin haka, ai kuwa itama taje ta rike Hajiya Lami ta matse ta gam tana kukan karya wai ta taimaka kar ta bari a tafi da su. Ita Hajiya Lami kokarin kwace kanta take saboda yadda taji Murjar ta riketa ji tayi kamar wani kato ne mai karfi a jiki ya matseta. Jan Zaki ne ya daka musu tsawa hade da cewa, "Kai shiiiit kuyi mana shiru, ku tashi ku biyomu in ba haka ba yanzu zan sa bindiga in kasheku na kashe banza". Murja ya nuna da bindiga ai kuwa a tsorace ta kara boyewa a bayan Mama Dije. Ita kuwa cikin sauri ta fincikota gaba, Murja kallonsu take daya bayan daya, gaba daya fuskokinsu babu annuri, da gani ba zasuyi imani ba. Wani ne ya zagayo ya buga mata kan bindiga a baya hade da cewa, "Maza ki tashi ko na harbeki yanzun nan". Cikin tsoro ta mike tsaye, yayin da itama Safuratu ta mike, yan fashin suka sa su a gaba sukayi hanyar fita bayan sun kwashe sarkokin da suka debo. Har sun kusan zuwa kofar fita, daya ya kalli Jan Zaki hade da cewa, "Oga tunda bamu sama kudi ba mai zai hana mu kwace wayoyinsu". Harara Jan Zaki ya galla masa bayan ya tsaya, sannan ya ce, "Wai kai Jangwal me yasa baka da hankali ne? Sau nawa ina fada maka, mu a satarmu bama karbar waya, ko ka manta wayoyin da muka taba sata aka bi didigi saura kadan mu shiga hannu? Ai ni bana harka da daukar waya musamman wayoyin masu kudi irin wannan, wasu idan ka dauka wayar da kanta zata tona maka asiri". Dan sadda kai yayi hade da cewa, "Gaskiya ne oga".
Suna fitowa daga falon, Biri dake dama a baya yake, ya koma cikin falon da gudu hannunsa rike da bindiga, su Hajiya Lami har sun fara dora hannu a kai sun dauka wani abu zaiyi musu. Yana zuwa sai ya dauki tukunyar kaza da Jan Zaki ya ci ya rage, hade da ledar chocolate din da ya daukko a dakin Jamsy yayi waje abunsa. Da sauri suka tura su Murja can kurya cikin mota, sannan suka duru a ciki suma, har zasu tayar da mota Jangwal ya ce, "Oga Biri bai fito ba fa". Zai daga baki yayi magana kenan, suka ga Biri ya fito da sauri hannunsa rike da tukunya dayan hannun kuma ya riko ledar chocolate da bindigarsa a hannu. Tsawa Jan Zaki ya daka masa hade da cewa, "Wai kai Biri wane irin maye ne kai? Dallah ajiye wannan tukunyar ka zo mu tafi". Kallon sauran naman kazar dake tukunyar yayi, Allah ya gani yana so, don haka ya ajiya tukunyar hade da daukar kazar sannan ya fada cikin mota. Tsaki Jan Zaki yayi, sannan ya ja motar yayi gaba. Suna wucewa, Sunusi ya bude murya hade da cewa, "Ihu barayi, ihu jama'a barayi". Bayan ya dauki katuwar sandarsa ya bi motar a guje. Mubarak da Hamza suma suka bi bayanshi suna ihu hade da daukar dutse suna jifan motar. Maza hudu ne kawai suka fito daga gidaje, lokacin tuni barayin sun bar layin. Sunusi ya tsaya yana maida yadda akayi yayinda Mubarak yayi cikin gida a guje, yana fadin bari aje a ga halin da su Hajiya ke ciki, sannan a kira yan sanda.
A bangaren su Hajiya Lami kuwa, yan fashin na fita Jamsy ta dafe kirji hade da cewa, "Wallahi wanda ya dawo din nan na zata harbinmu zaiyi da bindiga, ashe shi mayen abinci ne". Mama Dije ta ce, "Shegen ba, yan kajin da na sa ayi mun farfesunsu ne suka cinye, mayu kawai". Hajiya Lami ta ce, "Aje dai kajin ne rabonsu, yau na ga tashin hankali". Khalil ne ya tashi ya nufi hanyar saman bene da sauri, Hajiya Lami ta ce, "Kai ina zakaje haka da sauri?". Ya ce, "Mom waya zan daukko a kira yan sanda kafin yan fashin nan su yi nisa". Mama Dije ta ce, "Kai dawo dawo maza kyalesu suyi ta tafiya". Baya ya yo cikin rashin fahimta yana fadin, "Kamar ya a kyalesu?". Mama Dije ta ce, "Baka da hankali ne kai? Baka ga sun dauki wadannan aljannun yaran da suka addabemu sun tafi da su ba, a cewarsu wai mu hada kudin fansa million ashrin suka ce ko nawa?". Hajiya Lami ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Mama wallahi kamar kinsan abinda ke raina, wai million 20 suka ce mu hada domin su sako su Murja din, in ba haka ba wai zasu kashe su ta hanyar fyade". Mama Dije ma ta bushe da dariya sannan ta ce, "Banzaye basu san cewa mu masu iya biyan kudi ne a kashe mana yaran nan ba. Su je can su karata babu kudin da zamu hada, idan sun gaji da ajiyarsu sai su kashesu da fyaden". Sai a lokacin ne ma su Khalil din suka gane abinda iyayen nasu suke nufi. Jamsy ta ce, "Ai ni sai yanzu ma na gane abinda kuke nufi, dazun da nake a tsorace duk ban gane ba. Wallahi nima naji dadin dauke wannan mahaukaciyar". Mubarak ne ya fado a guje, yana shigowa ya fara binsu da idanu, "Hajiya ina fatan dai babu wanda ya rasa rayuwarsa, baku ji ciwo ba ko?". Hajiya Lami ta ce, "Mubarak ina barayin sun tafi ne?". Mubarak ya ce, "Eh wallahi Hajiya har sun tafi, mun bisu a guje ma dake a mota ne bamu iya kamo su ba, na ga kamar sun tafi da wasu ko? Don Allah a kira yan sanda Hajiya, nasan idan ba'a makara ba ana iya isko su a ceto wanda suka sata". Mama Dije ta ce, "Kai rabu da su, dama ba wasu mutanen kirki ne suka dauka ba fa, su Murja ne, kuma dama mu mun rasa yadda zamuyi mu koresu daga gidan nan, kaga kuwa Allah ne ya kawo mana hanyar rabuwa da su a saukake". Tafe suke a mota..................
☹️ Ni kuma na ce ba zan bi su ba in kona man babur dina, gashi mai yayi tsada
Muje zuwa
Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group
Wa.me/+2348096831009
😍